- Lamarin ya faru ne a jihar Oyo, kuma hukumar 'yan sandan jihar ta yi holinsu
- Man dai har yanzu yana wahala, wanda hakan ke nufi akwai riba in an sayar ta barauniyar hanya
An kama wani kurtun soja da abokansa masu harkar mai sun juya akalar wata tankar mai. Lamarin ya faru ne a jihar Oyo, kuma hukumar 'yan sandan jihar ta yi holinsu.
Kwamishinan yansandan jihar ne ya yi holinsu a ofishinsa a jihar ta Oyo a garin Ibadan, sojan sunansa Akpan Edet dan shekaru 28.
Cikin wadanda ake shirin kaiwa kotun a lokacin sun kai kimanin 18, kowannensu kuwa anyi hotonsa da daukar zanen yatsunsa.
Man dai har yanzu yana wahala, wanda hakan ke nufi akwai riba in an sayar ta barauniyar hanya. Farashin lita ya kan tashi daga n145 zuwa n400 ko fi ma.
An gano cewa wasu ne ke boye man ko chanja masa akala, daga gidajen mai zuwa lunguna domin sayarwa a kasuwar bayan fage ta black market.





0 Comments:
إرسال تعليق