A yayin da muke bankwana da shekarar 2017, shafin ArewaTop.com yayi waiwaye inda ya kawo muku wasu daga cikin jarumai da mawaka na fina-finan Hausa da suka tsallaka zuwa kasashen waje a wannan shekarar.
Zamu fara da Ali Nuhu(Sarki), a wannan shekarar jarumin yaje kasar Ingila, inda ya yiwa Jaruman fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi da Ramadan Booth jagora suka karbi lambobin yabo acan.
Haka Kuma Alin yaje kasar Turkiyya inda daga nane ya dawo gifa Najeriya.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Halima Atete taje kasar Saudiyya inda ta sauke farali, akayi aikin hajjin bana da ita. Haka kuma jarumar taje kasar hadaddiyar daular larabawa jawan shakatawa da kuma kasar Turkiyya.
A farkon wannan shekararne, Korarriyar , fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau taje aikin Umrah ita da 'yan gidansu, haka kuma jarumar taje kasashen, hadaddiyar daular larabawa, Turkiyya da kasar Cyprus wadda har yanzu tana can bata dawo ba.
A wannan shekarar, Nafisa Abdullahi taje aikin Umrah sannan kuma taje kasar Ingila inda ta amso kyautar kartamawar da aka mata.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon taje yawan shakatawa kasashen hadaddiyar daular larabawa, da kuma kasar Amurka a cikin wannan shekarar.
A wannan shekarar ne tauraron fina-finan kuma mawaki, Adam A. Zango yaje kasar Kamaru inda aka mishi taron da ba'a taba yiwa wani jarumi ko kuma mawakin fim din Hausaba, kamar yanda Adamun ya bayyana, yace kimanin mutane dubu gomane suka taru don kallonshi a kasar ta kamaru, kuma koda a cikin bidiyon da yayita yawo na ziyarar taahi a kasar ta Kamaru, za'a iya ganin dandazon mutane sunata shewa da murnar ganin Adamun.
A wanan shekarar, Tauraron fina-finan Hausa, Sadik Sani Sadik yaje kasar Kamaru inda shima ya nisha dantar da masoyanshi acan.
Jarumin fina-finan Hausa, Ramadan Booth yaje kasar Ingila a wannan shekarar inda ya amshi kyautar karramawa da aka nashi acan.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rukayya Dawayya taje aikin Umarah a wannan shekarar.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samira Ahmad itama tace aikin umrah a wannan shekarar.
A'isha Tsamiya itama taje aikin Umrah a wannan shekarar.
Baban Cinedu yaje aikin Hajji a wannan shekarar.
Musa Mai Sana'a yaje aikin Hajji a wannan shekarar.
Salisu Fulani yaje kasar Saudiyya sauke aikin Umrah.
Fati Muhammadd taje aikin Umrah a wannan shekarar.
Aminu Alan waka shima yaje aikin Umrah a wannan shekarar.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa taje aikin Umrah a wannan shekarar, haka kuma taje kasar Nijar duk a wannan shekarar.
Jarumar fina-finan Hausa, Sa'adiya Kabala taje aikin Umrah a wannan shekarar.
Jarumar fina-finan Hausa, Khadija Mustafa take aikin Umrah a wannan shekarar.
A karshe kuma sai jarumin fina-finan Hausa, Mustafa Nabaraska da shima yaje aikin Umrah a wannan shekarar.
0 Comments:
إرسال تعليق