Karanta Sabbin Tsarukan Da Aka Sanya ma Facebook
Kamfanin Sada Zumunta na Facebook ya kaddamar da sabbin tsare-tsare da za su bai wa masu amfani da shafinsa damar kare bayanansu na sirri cikin sauki.Wannan na zuwa ne bayan an kwarmato cewa, kamfanin ya yi wa mutane miliyan 50 kutse, abin da ya haifar da cecekuce a sassan duniya.
Sabbin tsare-tasren da Facebook ya kaddamar za su bai wa masu amfani da shi damar shiga cikin bayansu na sirri don sauya abin da suke so cikin sauki tare da sauke ko kuma share wasu bayanai da kamfanin ke adanarsu.
Kazalika kamfanin ya ce, tsare-tsaren za su bai wa jama’a damar kare bayanansu da kansu, in da za su rika zabar irin mutanen da suke so su rika duba bayanansu a shafin tare da dakatar ko kuma barin tallace-tallacen da ke bijirowa a shafukansu.
Shgaban sashen kare bayanan sirrin jama’a a Facebook, Erin Egan ya ce, sun samu bayanan da ke cewa, mutane na shan wahala wajen lalubo wuraren da za su latsa don kare bayanansu, abin da ya sa ya ce, ya zama dole su wayar da kan al’umma.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan kamfanin ya sha zazzafar suka jim kadan da samun labarin yi wa mutane miliyan 50 kutse a kundinsu, lamarin da ake ganin yana da nasaba da yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.
Ko da dai shugaban kamfanin na Facebook, Marc Zuckerberg ya fito ya bada hakuri kan abin da ya faru, amma duk da haka ‘yan Majalisun Amurka sun bukace shi da ya bayyana a Washington don bada bayani kan batun.
Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi daukan mataki nan gaba kan kamfanin, in da tuni Birtaniya ta kaddamar da nata binciken.
0 Comments:
إرسال تعليق