An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari
Wata Kotu a Kasar Indiya ta yankewa shahararen jarumin finan-finan Indiya Salman Khan hukuncin zaman shekaru biyar a gidan yari saboda laifin kashe wasu dabobi wadanda basu da yawa a duniya a wata farauta da yayi.
Lauya mai shigar da kara, Mahipal Bishnoi ya shaidawa manema labarai a birnin Rajasthan da ke Jodhpur cewa: "Kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar rupees 10,000 ($150)."
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Lauyan ya cigaba da cewa a yanzu ana shirye-shiryen kama jarumin mai shekaru 52 a duniya don tisa keyar sa zuwa gidan yari na garin Jodhpur.
Sai dai Salman Khan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma yana da damar daukaka kara a wata kotun.
An Bayarda Belin Salman Khan
0 Comments:
إرسال تعليق