A RANAR Asabar ɗin wannan makon, wato 14 ga Afrilu, 2018, za a ɗaura auren ɗaya daga cikin jarumai mata da ke Kaduna, wato Sadiya Kabala.
Za a ɗaura auren ta da sahibin ta mai suna a masallacin Juma'a na Al-Mannar da ke Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
A jerin tsarin bikin wanda mujallar Fim ta gani, an nuna cewa za a fara shagalin auren a ranar Alhamis ɗin nan a lambun shaƙatawa na Ƙofar Gamji.
Bayan ɗaurin auren kuma za a yi dina a wani otal mai suna Silver Sand da ke Titin Katuru, Unguwar Sarkin Musulmi.
To Allah ya sa a ce gara da aka yi, amin.
0 Comments:
إرسال تعليق