MARYAM Saleh (Fantimoti) mawakiya ce da ake yi mata lakabi da Maman Mawaka. Hakan babu mamaki saboda tsawon lokacin da ta shafe a harkar waka, domin kuwa za a iya cewa kusan duk mawakan da ke waka a yanzu da ma wasu wadanda su ka gabace ta a Kannywood sun yi yayin su sun gama, amma ita har anzu ana damawa da ita. Ta yi wakoki a fannoni daban-daban kamar na soyayya, na yabon Manzon Allah (S.A.W), na siyasa, da sauran su.
Wani abu game da Maryam shi ne a duk lokacin da ake ganin kamar an daina yayin ta, sai kuma a gan ta ta fito da wasu sababbin wakoki da ake sakawa a cikin finafinai. Tun daga fitowar fim din 'Mansoor' wanda ya ke dauke da wakar ta, sai kuma aka koma kan ta, kowa na so ya rera masa wakar fim din sa.
Wakilin mu, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da Fantimoti a Kano a game da yanayin da ta ke ciki, musamman a bangaren waka. Ta fede mana biri har wutsiyar sa kan sirrin waka:
Wani abu game da Maryam shi ne a duk lokacin da ake ganin kamar an daina yayin ta, sai kuma a gan ta ta fito da wasu sababbin wakoki da ake sakawa a cikin finafinai. Tun daga fitowar fim din 'Mansoor' wanda ya ke dauke da wakar ta, sai kuma aka koma kan ta, kowa na so ya rera masa wakar fim din sa.
Wakilin mu, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da Fantimoti a Kano a game da yanayin da ta ke ciki, musamman a bangaren waka. Ta fede mana biri har wutsiyar sa kan sirrin waka:
FIM: Maryam Fantimoti, ki na cikin mawakan da su ka dade a cikin wannan masana’anta ta Kannywood, ko da yake tsawon lokaci ba a jin ki sosai. Wannan ta sa ake ganin kamar kin ja baya a harkar waka. Yanzu kuma sai aka fara jin muryar ki. Wannan ya sa ake ganin kin dawo kenan daga hutun da ki ka tafi.
FANTIMOTI: To, assalamu alaikum. Wannan maganar da ka fada za a iya cewa haka ne, domin ka san ita waka ta na tafiya ne da zamani, domin ni lokacin da na shigo masana'antar akwai raino. Ka ga ni Ali Nuhu ne ya karbe ni kuma ya gwada ni da wannan wakar mai suna ‘Fantimoti’, wadda har zuwa yau na ke amsa sunan ta. Don haka lokacin akwai yarda da amana, ba kamar yanzu ba.
To lokacin da na yi wannan wakar Ali Nuhu ya kai wa marigayi Tijjani Ibraheem sai ya ce, “Wannan muryar babu irin ta, don haka an samu canjin Zuwaira Isma’il!” Ka san ni muryar Zuwaira na ji na shigo waka lokacin da su ka yi wakar ‘Dawayya’ ita da Misbahu M. Ahmad. To ita ta jawo ni, don na ga ni ma fa mawakiya ce a Islamiyya, don haka ni ma zan iya. Amma ni kuma sai na zo da salo na tatsuniya; da na rubuta na kawo wa Ali Nuhu sai ya ce ai ni murya ta ita ce makami na. Don haka tun daga nan zan iya ce maka ban kara waiwayar biro ko takarda ba don na rubuta waka, sai dai duk inda ka gan ni kawai rera ta zan yi.
To, da yake akwai kulawa ta magabata sai na ci gaba da samun nasara, don ka ga bayan Yakubu ya raine ni sai Mudassiru ya dora. Allah Ya saka musu da alheri; ba zan iya mantawa da su a tarihin rayuwa ta ba.
FIM: Akalla shekara nawa kenan daga wancan lokacin zuwa yanzu?
FANTIMOTI: E to, shekarun da dan tafiya ba laifi, domin na shigo masana’antar fim tsakanin 1999 ko 2000, don haka ka ga ai na dade a cikin harkar.
FIM: A tsawon wannan lokaci, kin yi wakoki kala-kala. Bayan wakar 'Fantimoti' da ta fito da ke, za ki iya tuna wasu fitattun wakokin ki?
FANTIMOTI: Wato lokacin da na zo masana’antar gaskiya an fi yin waka a kan abin da ya danganci fim din, ana yin waka daidai da yadda sakon labari ya ke, don haka labarin fim din ake dauka a yi waka, wanda kuma a yanzu ba haka ba ne. Don ba zan manta ba, akwai wakar da na yi ta fim, da Maryam ta zo yin wakar a fim din sai da ta yi kuka na gaske a fim din saboda tausayin da ya ke cikin wakar. To yanzu waka ta juya soyayya kawai, amma mu a da ba haka ba ne.
FIM: Wakoki ku na da sun fi daukar dogon lokaci ana yayin su fiye da na yanzu. Me ya jawo haka?
FANTIMOTI: E to, ya danganta. Ka san ita waka ta na da matakai, domin idan Allah Ya hore maka waka matakin ta na farko shi ne murya, sai kuma basira. Idan ka na da murya ba ka da basira, za kai waka kuma za ka ci abinci. Sai kuma balaga, wato saka maganganun da zai fito a ciki. Sai kuma shirya baitocin. Sai kuma daukaka da karbuwa, yadda zai zama kowa ya san ka.
FIM: Wato kenan wannan shi ne ya bambanta mawakan da da na yanzu?
FANTIMOTI: E, gaskiya ne. Ka san lokacin da su Yakubu da su Mudassiru su ke waka gaskiya ba za a yi waka ba sai da ma’ana. Wannan ya sa ta dalilin raino na da su ka yi yanzu da manyan mutane na ke mu’amala. Saboda manyan mutane su na so su ji abubuwa na al’ada a cikin waka, kuma a yanzu waka mun saki al’ada.
FIM: Bayan tsawon lokaci ki na wakokin finafinai, sai kuma ki ka karkata akala wajen wakokin yabon Manzon Allah (S.A.W.), kuma sai ya zama a wannan bangaren ma ki ka shahara kamr da man a nan ki ka fi kwarewa.
FANTIMOTI: Wannan gaskiya ne, amma abin da ka fada ba haka ba ne. Lokacin da mahaifi na ya kai ni Islamiyya shekara ta takwas, to a lokacin a kan tebur malamai ya ke dora ni na yi kasida a cikin ajin mu, don haka tun a lokacin aka koya min son Manzo da kuma yin yabo a gare shi. Hakan ya sa na samu mukami a makarantar, don malami zai zo da kasida ya na biya mana, amma sai ya ji na haddace. Tun daga nan na fara iya yabon Manzon Allah (S.A.W.), amma yanzu abin bayyana ya yi.
FIM: Yaya za ki kwatanta wakoki na yabon Manzon Allah da kuma na finafinai da ki ke yi? Wanne ne ya fi sauki?
FANTIMOTI: E, a wajen rerawa daya ne, amma a wajen da bambancin ya ke shi ne wakokin yabon Manzon Allah gaskiya sai ruhi ya amsa. Idan ruhi ya amsa kuma ka yi ladabi, to idan aka samu wannan shi ne za ka ji yabo ya karbu.
FIM: Akwai wani lokaci da ake korafi kan masu wakokin yabo, ana cewar ba su cika yin lafazi na isar da sako a cikin wakokin su ba.
FANTIMOTI: Wannan haka ya ke. Wato idan Allah Ya yi baiwar rera waka, to shi gida na yabo dole sai dai ka je ka yi ladabi a ba ka. Amma idan ka ce za ka yi don ka na da murya, to akwai matsala. Ka’ida shi ne: ka je malamai su ba ka. Kamar yanzu idan ka ji wakar ‘Mukarrima’ za ka san cewa ta fi karfin kai na, ba ni aka yi yi, wato waka ta da na ke cewa: “In ba ka gane me mu ke nufi ba ku ce da su mu na nufin Ma’aiki.” To ka san abin ya fi karfin kai na, don haka malami na, maulana Malam Hafiz Abdallah, shi ne ya ba ni wannan kasida na rera.
Don haka duk lokacin da za ka yi wake na yabon Manzon Allah (S.A.W.) ka je ka yi ladabi ko ka je wajen masu abin, Ahlul Baiti - jikokin Manzon Allah - su ba ka. Lamarin da ake fada da izini domin su fa gaske ne ko a lahira bare a duniya. Don haka idan su ka ba ka lamuni, in ka yi yabon sai an saurare ka.
Amma don kawai ka iya wakar fim ka ce za ka yabi Manzon Allah, to akwai matsala. Sai dai ka yarda malamin ka ya ba ka. Don a kasashen da su ka ci gaba za ka ga marubuta waka daban, masu rerawa daban. Ba kamar mu nan ba, mutum ya ce shi ne kida, shi ne rubuta waka, shi ne rera waka.
FANTIMOTI: Wakar ki ta fim din ‘Mansoor’ ta kara dawo da ke wakokin finafinai. Ko yaya ki ka kalli yadda tsarin wakar ya ke a yanzu?
FANTIMOTI: A wannan yanayi dai ba zan iya cewa komai ba domin ba da kowa na ke rera waka a cikin yaran da su ke tashe a yanzu ba, domin zan iya cewa kai ni ban taba yin waka da su ba! Don ban yi waka da Nura M. Inuwa ba, ban taba yin waka da Umar M. Shareef ba. Amma na yi waka da Ado Gwanja, Hussainin Danko, Rarara, Nazifi Asnanic, Sani Hassan, Mahmud Nagudu, duk na yi waka da su.
To abin dai da ya faru su mawakan ne yanzu da su ke cewa da ni Maman Mawaka, an ba ni lambar yabo an ce da su ba za su iya biya na kudi ba, na raina musu waka. To ni abin da zan warware musu, ni har abada a harka ta ta waka na dauki mawaki ko yau ya fara waka abokin sana’a ta ne; zan taimake ka, za ka taimake ni. Kuma na gode wa Allah da Ya raba ni da girman kai. Don haka su ajiye wannan lissafin. In ka na so a yi maka wakar ma ka zo za a yi maka ka rike kudin ka, don mu ba abin da Allah bai yi mana a cikin ta ba.
FIM: Ko wadanne irin nasarori ki ka samu a harkar waka?
FANTIMOTI: To, nasarorin su na da yawa. Nasara ta farko ita ce zama da dukkanin mawaka lafiya. Na samu nasara ta fahimtar iyayen gida na a harka ta waka. Na samu nasara ta daukaka ta ba iya kasa ta ta tsaya ba, tunda cikin ikon Allah na fita aiki kasashen makotan mu kamar Nijar, Chadi, Kamaru, Ghana, Togo.
FIM: Wanne irin kalubale ki ka fuskanta a harka ta waka?
FANTIMOTI: E to, ka san ita rayuwa ba a raba ta da kalubale, don tun daga gidan ku da aka haife ka ba ka rasa kalubale. Amma kalubalen da ya fi damu na shi ne rashin hadin kan mawaka. A matsayin mu na ’yan’uwan juna ya kamata mu hada kai mu yi aiki tare. Wannan shi ne abin da ya kamata mawaka su yi.
FIM: Menene sakon ki na karshe?
FANTIMOTI: To, shi ne dai maganar hadin kai. Ina kara kira ga mawaka mu hada kai mu yi aiki tare yadda za mu zama masu daraja sana’ar mu
0 Comments:
إرسال تعليق