Saudiyya Ta Yi Nasarar Soke Wasannin Sharholiya Da Aka So Shiryawa A Kasar
Bayan taron gaggawa da ya gudana tsakanin Yerima mai jiran gado kasar Saudiyya da membobin majisar koli ta
manyan malamai a gidan ministan al’amuran addini Sheikh Saleh bin Abdul’aziz gwamnatin ta soke shirin kida da wasa da mata wanda za a gabatar a Riyad. Sannan kuma ta soke taron da mawakiyar nan Majidatu Alrumy 'yar kasar Lebanon za ta gabatar a jami’ar Gimbiya
Nuratu a Riyadh.
Ta kuma soke taron mawakin nan Khazeem Saheer dan kasar Iraq. Haka kuma ta rufe wurin shakatawa a garin Jazan sakamakon cakuda maza da mata a wajen taron wata gala.
0 Comments:
إرسال تعليق