الثلاثاء، 8 مايو 2018




Motar banki ta zubar da kudi sama da N215m akan babbar hanya sakamakon kofar data bude suna cikin tafiya basu sani ba (hotuna)

Home Motar banki ta zubar da kudi sama da N215m akan babbar hanya sakamakon kofar data bude suna cikin tafiya basu sani ba (hotuna)

غير معرف

Ku Tura A Social Media


- Motar banki ta barar da kudi a Indiya, kusan $600,000, wanda yayi daidai da naira miliyan 215 ‘yan kwanaki da suka wuce sakamakon kofar motar ta bude bisa kuskure

- Lamarin ya faru ne sakamakon kofar baya ta motar data bude direbobin basu sani ba akan hanyarsu na kai kudade a jihohi daban-daban

- Direban bai fahimci abunda ke faruwa ba sai bayan wani direba ya daga masa hannu yana nuna masa bayan motarsa

Motar banki ta barar da kudi a Indiya kusan $600,000, wanda yayi daidai da naira miliyan 215 ‘yan kwanaki da suka wuce sakamakon kofar motar ta bude bisa kuskure.

Lamarin ya faru ne sakamakon kofar baya ta motar data bude direbobin basu sani ba akan hanyarsu na kai kudade a jihohi daban-daban, inda jikkunan kudi da rafofin kudi suka dinga fita ta baya suna bin iskan kafin motar ta tsaya.

Direban bai fahimci abunda ke faruwa ba sai bayan wani direba ya daga masa hannu yana nuna masa bayan motarsa.

'Yan Sanda sun gaggauta zuwa wurin don su tsince abunda ya samu, saboda kafin ma su karaso wasu direbobin sun tsaya sun fara dibar rabonsu da kuma mutanen garin dake kusa suka sun rugo suna dibar nasu rabon.

Source naij.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: