Rahama Sadau Ta Bada labarin Yadda Ta Rasa Budurcin Ta
Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta
- Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin fira da majiyar mu a satin da ya gabata
- Ta ce an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama ne
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Rahma Sadau ta yi karin haske game da yadda ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba bada labarin cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba a watannin baya.Jarumar dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take yin fira da majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata karon farko tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda taje karatu.
Jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba wai tana nufin ta taba zina ba ne domin ita hasali ma ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.
Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.
الثلاثاء، 29 مايو 2018
Author: غير معرف verified_user
RELATED STORIES
Kalli hoton AlaAlan waka da ado gwanja a wajen taron ........Kalli hoton AlaAlan waka da ado gwanja a wajen ta
Kalli Wasu Sabbin Hotunan Fati Washa Wanda Suka Ja Hankulan Mutane.Kalli Wasu Sabbin Hotunan Fati Washa Wanda Suka J
Kalli wasu zafafan hotunan maryam yahaya wanda suka birge mutabe sosai. Kalli wasu zafafan hotunan maryam yahaya wanda su
Kalli wani kayatattan hoton maryam gidado wanda ya ja hankulan mutane. Kalli wani kayatattan hoton maryam gidado wanda y
Jibi wasu kayatattun hotunan fati shu,uma wanda suka ba mutane mamaki sosai. Jibi wasu kayatattun hotunan fati shu,uma wanda s
Kallo wasu hotunan maryam gidado wanda suka janyo mata abin magana. Kallo wasu hotunan maryam gidado wanda suka janyo
0 Comments:
إرسال تعليق