A yayin da zaben shekarar 219 ke kara matsowa, 'yan takarar kujeru daban-daban na kara fitowa domin nuna sha'awar su ta yin takara a jam'iyyun kasar nan.
Duk da korafin da mata keyi na ba basu dama a siyasance kamar yadda ya kamata, wasu mata sun bugi kirji sun fito domin a dama da su.
1. Dakta Salma Kolo
Tsohuwar kwamishiniyar lafiya a jihar Borno ta fito domin karawa da Sanata Ali Ndume a takarar kujerar Sanatan jihar Borno ta kudu a karkashin jam'iyyar APC.
2. Binta Binta: Tsohuwar kwamishiyar mata a jihar Gombe ta bayyana niyyar ta na tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai a mazabun Kaltungo!Shongom a karkashin jam'iyyar PDP.
3. Mimi Adzafe-Orubibi: Shugabar hukumar tattara haraji ta jihar Benuwe na son tsayawa takarar kujerar Sanata wacce yanzu tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Barnabas Gemade, ke kai.
4. Sanata Bamisola Saraki: Har yanzu tana sha'awar tsayawa takarar gwamnan jihar Kwara duk da ta sha kaye a takarar kujerar a 215.
Bamisola, kanwa ce wurin shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki, kuma yanzu ta dawo jam'iyyar APC.
5. Sanata Rose Oko: Sanata mai wakiltar jihar Kuros Riba ta Arewa ta bayyana niyyar ta na sake tsayawa takara a zabe mai zuwa duk da yawan masu son maye gurbin ta.
6. Fasto Margaret Inusa: Duk da bata yi fice a tsakanin 'yan siyasar Najeriya ba, Margaret zata tsaya takarar gwamna a jam'iyyar ADP tunda gwamnan jihar, Simon Lalong, zai kara tsayawa takara a jam'iyyar APC.
7. Aisha Dahiru Ahmed: Tsohuwar mamba a majalisar wakilai daga jihar Yola karkashin jam'iyyar PDP da yanzu ta koma APC inda take burin yin takarar kujerar Sanatan jihar Adamawa ta tsakiya, kujerar da ta fadi zaben ta a shekarar 215 a karkashin jam'iyyar PDP.
Hausa.naija.ng
0 Comments:
إرسال تعليق