الأحد، 17 يونيو 2018




GUDUN MAWAR RONALDO GA MUSULMAI

Home › › GUDUN MAWAR RONALDO GA MUSULMAI

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Dan kwallon kasar Portugal mai wasa a kungiyar Real Madrid, Christiano Ronaldo shine wanda ya ki karbar tallar da kamfanin lemon kwalba na Pepsi suka ba shi, saboda ya zargi kamfanin na Pepsi da tallafawa sojojin kasar Isra'ila da kudin sayen makaman da suke cin zarafin Falasdinawa musamman yara kanana.
Haka kuma Ronaldo ya ki amincewa ya yi musanyar riga da 'yan kwallon kasar Isra'ila a wani wasa da suka buga saboda a cewarsa ba zai yi musanyar riga da masu kisa ba.
Haka kuma bayan gudummawar takalmin gwal din da Ronaldo ya baiwa yaran Falasdinawa da aka raunata, ya kuma tarbi wasu 'yan gudun hijirar Siriya da suka shigo kasar Spain hannu bibiyu.
Fatan mu Allah ya Musuluntar da shi domin ya dora daga inda ya tsaya.
Ko a lokacin da Ozil yake wasa a Madrid yakan koyawa Ronaldo wasu daga cikin ayoyin kur'ani saboda sha'awar da yake yi wa musulunci.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: