الأربعاء، 25 يوليو 2018




[Audio Album] :- sabon Album ( Manufarmu ) from Abnur House 2018

Home [Audio Album] :- sabon Album ( Manufarmu ) from Abnur House 2018

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Sabon album din da ya fita kwana biyu da suka wuce na manyan mawaka tare da matasan mawaka mai suna ” Manufarmu ” Wanda Kamfanin Abnur Entertaiment ta dauki nauyin saki duk tsakiyar shekar karkashin mawaki nura m inuwa.
Dalilin yin wannan album mawaki nura m inuwa yace”
Kamar yadda nasan ban isa  na daukaka wani ba, Haka na yarda ban isa na  durkusar da wanda Allah  yaso ya daga ba.
Ina mai farin cikin bayyana muku wannan poster a matsayin sabon Album dinmu na tsakiyar shekar  wanda na yanke shawarar zan dingayinsa da mawaka a ko wace tsakiyar shekara saka makon korafin masoyana na rashin sakin Album Akai Akai  da banayi , wannan shirine musamman dan bada gudunmawa ga yan uwana mawaka badan nura ya isaba ko kuma na kai kaina wani guri ba.
Manufarmu itace kowa yasan da babu dan koyo  da ba a sami gwani ba, salon zaici  gabane har zuwa kan mawakan dama  ban sansu ba indai sunda basira.
A karshe ina mai jan hankalinmu da mu dogara ga Allah akan komai.
SUNAN MAWAKAN DA SUKE CIKIN WANNAN ALBUM DIN:-

1- Nura M Inuwa 2- Annur H Banur 3- Faruk M Inuwa 4- Shamsu Alale 5- Anas A Ibrahim 6- Sani B haruna 7-Ali Show
Gamai bukatar wannan Album to ya garzaya kasuwa domin siyan dai dai ko sari.
GA Waka daya daga ciki ku dandanata.
Audio Player
00:00
00:00


Source :- Arewablog.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: