الاثنين، 2 يوليو 2018




SO NE... PART 3

Home SO NE... PART 3

غير معرف

Ku Tura A Social Media


Ina bude message na farko naga ta turomin adress nata ne, dakuma cikakken sunanta Fatima Bulama, sannan kuma daga kasa akwai hotunanta guda uku, tsayawa nayi na kasa motsi ina kallon hoton nata, ba komaine yasa ba sai saboda tsananin kaywun ta.
Fatima ta kasance kyakykyawar mace ta gaban kwatancen mai kwatance, sannan ta kasance black beauty ce amma ba baka can ba, bakin ta ya kasance madaidaici wato chocolate colour ce wanda duk wanda ya ganta sai yaji inama ace shine zai aureta, inanan zaune na kasa motsi sai kallon fuskar Fatima kawai nakeyi wanda a lokacin naji na fada cikin tunani.
saida na shafe kimanin mintuna 10 ina zaune ina kallon hoton, sannan na fito daga message din, na bude na biyun, ba komai na ganiba a cikinsa sai sako daga MTN mai cewar an saka mini credit a waya ta na naira dubu biyu, na duba lambar da aka turomin sai naga lambar Fatima, a lokacin ne na fara zargin anya kuwa Fatima ba wata manuface a ranta ba? Amsar da na kasa baiwa kaina kenan, haka na fito daga cikin dakina naje na gaishe da iyayena sannan na fita waje domin zuwa wajen karyawa.
Haka na wuni cikin rashin sukuni a wannan rana, koda wanne lokaci na zauna sai tunani, abokina Aji ya tambayeni shin menene ke damuna yau gaba daya na chanza, sai nacemasa bakomai, haka ya gaji da tambaya ta nikuma naki fada masa komi saidai nacemasa bakomai, haka ya hakura amma bai gamsu da amsar da na bashi ba.
Lokacin da dare yayi naje na kwanta na dauki wayata na bude facebook ina chat da abokaina har bacci ya fara dauka na, sai na ajiye waya ta akan tebur sannan na kwanta domin nayi bacci sai baccin ya gagareni sai tunanin Fatima, ina cikin hakan ne naji wayata tana ringing

Share this


Author: verified_user

0 Comments: