INEC ta kaddamar da zaben Kastina ta Arewa domin maye gurbin kujeran a majalisae dattawa
- Ana gudanar da wannan zabe ne sakamakon rasuwar Sanata Mustapha Bukar wanda ke wakiltan mazabar
- Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranan Alhamis ya garzaya Daura domin yakin neman zaben jam'iyyar APC
An fara zaben kujerar sanatan Katsina ta Arewa cikin zaman lafiya da lumana a kananan hukumomi 12 da ke karkashin mazabar a ya Asabar, 11 ga watan Agusta 2018.
NAIJ.com ta samu labarin cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun kaddamar da zaben kuma mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu.
Game da cewar NAN, an fara tantance masu zabe misalin karfe 8:00 na safe kuma jami'an INEC sun isa da wuri.
Mutane sun fito kwansu da kwarkwatnsu domin zabe tsakanin yan gida daya dake takarar kujera daya. Kabir Babba Kaita na jam'iyyar PDP da kaninsa, Ahmad Babba Kaita na jam'iyyar APC
Wani dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yabawa hukumar INEC bisa ga isowarsu da wuri. Yace an fara zabe a unguwanni 148 da ke mazabar a lokaci daya.
Mazabar Katsina ta Arewa ya kunshi kananan hukumomi Daura, Maiadua, Zango, Sandamu, Baure, Mani, Mashi, Dutsi, Ingawa, Bindawa, Kankiya da Kusada.
0 Comments:
إرسال تعليق