Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga
takwarorinsa na kasashen duniya a babban taron
Majalisar Dinkin Duniya a New York, Amurka,
ranar Talata, inda zai tafi tare da matarsa da
wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada
ministoci da gwamnoni.
Shugaban zai bar Najeriya ne ranar Lahadi domin
halartar babban taron na karo na 73, wanda aka
bude tun ranar Talata 18 ga watan nan na
Satumba.
Ana sa ran Buhari zai jaddada matsayin kasarsa
kan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya
da wanzar da cigaba mai dorewa na tattalin
arziki da zamantakewa da watsi da makaman
nukiliya da samar da aiki ga matasa da mata, da
batun sauyin yanayi da tabbatar da bin doka da
oda da sauransu.
Ana kuma ganin shugaban na Najeriya zai nemi
kasashen duniya su mayar wa kasarsa kudadenta
da aka sace aka kai kasashensu, tare da neman
goyon baya ga yakin da gwamnatinsa ke yi da
cin hanci da rashawa.
Zai kuma bukaci da a sake fasalin kwamitin tsaro
na Majalisar ta Dinkin Duniya, game da
mambobin dindindin, ta yadda zai zamanto yana
da wakilci na nahiyoyin duniya daban-daban.
Na yanke hukunci kan takarar Buhari a 2019
— Aisha Buhari
Matasan Najeriya 'sun fusata' da kalaman
Buhari
Kun san cutar da ke damun Muhammadu
Buhari?
Shugaba Buhari da tawagar tasa za su halarci
wani babban taro da za a yi a kan yaki da tarin-
fuka wanda hukumar lafiya ta duniya za ta
shirya, kasancewar kasar ita ce ta bakwai a
tsakanin wadanda cutar ta fi yawa a cikinsu a
duniya kuma ta biyu a Afirka.
Shugaban da matsarsa A'isha za su halarci
liyafar maraba wadda Babban Sakataren
Majalisar Antonio Guterres da matarsa za su
shirya wa shugabannin kasashen duniya da
matansu.
0 Comments:
إرسال تعليق