Kotun koli a Indiya ta halatta yin luwadi da madigo a kasar, matakin da aka dade wasu na adawa da shi.
Kotun ta halatta yin hakan ne ga manya da suka mallaki shekarun girma.
Hukuncin dai ya yi wa masu gwagwarmayar kare 'yan luwadi da madigo dadi inda suka rungumi juna suna murna bayan zartar da hukuncin.
Alkalai biyar ne suka yi nazari game hukuncin da ya yi watsi da hukuncin da ya haramta luwadi da madigo a shekarar 2013 bisa dokar zamanin turawan mulkin mallaka.
Tsohuwar dokar tun zamanin turawan mulkin mallaka da aka fi sani da sashe na 3-7-7 ta zartar da hukuncin duk wanda aka samu da yin madigo da luwadi za a yanke masa hukuncin ko dai sama da shekara 10 a kaso.
A yanzu kotun ta yanke hukuncin cewar nuna wariya bisa game da irin nau'in jima'in mutum toye hakkin dan Adam ne.
Tun da farko ma su fafutuka sun ce ayyana auren jinsi a matsayin laifi, zai zama babbar barazana ga 'yancin masu ra'ayin auren jinisi daya.
0 Comments:
إرسال تعليق