السبت، 29 سبتمبر 2018




TABBATAR DA MUTUWAR MUTUM380BAYAN DA BALA IN TSUNAMI TARE DA GIRGIZAR KASA

Home › › TABBATAR DA MUTUWAR MUTUM380BAYAN DA BALA IN TSUNAMI TARE DA GIRGIZAR KASA

غير معرف

Ku Tura A Social Media
 tabbatar da mutuwar mutum 380 bayan da
bala'in tsunami tare da girgizar kasa mai karfin
maki 7.5 ta afka wa wani babban birnin a kasar
Indonesia a ranar Jumma'ar da ta wuce.
Igiyoyin ruwa sun yi tunkoro har zuwa tsayin
tsayin mita uku hakan ya sa ruwa ya shafe
tsibirin Sulawesi.
Hotunan bidiyon da aka sanya a kafafan sada
zumunta sun nuna yadda mutane ke ta kururuwa
tare da tserewa a cikin dimuwa.
Dubban gidaje da asibitoci da ote-otel da kuma
shaguna ne suka rushe sakamakon girgizar
kasar.
Masu aiki ceto na ta kokari wajen ceto mutane
da lamarin ya rutsa da su, koda yake suna
fuskantar 'yan wasu matsaloli a aikin ceton na
su.
An rufe babbar hanyar da ta bulla zuwa birnin
Palu saboda zaftarewar kasa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce
akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa ransu
sakamakon girgizar kasar zai iya karuwa, kuma
akwai mutum akalla 540 da suka samu raunuka,
yayin da kuma ba a gano wasu mutum 29 ba.
Mai magana da yawun hukumar agajin
gaggawan, Sutopo Purwo Nugroho ya shaida wa
kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, an
gano wasu gawawwakin a gefen gabar teku.
Ya kuma ce koda al'amarin ya fara faruwa sama-
sama a ranar Jumma'ar, mutane sun ci gaba da
harkokinsu a bakin ruwa, amma kuma da lamarin
ya munana sai suka fara tserewa.
Wasu mutane dai sun tsira da ransu ne bayan da
suka dirgo daga wani gini mai nisan mita shida.
A Palu, daruruwan mutane ne suka shirya shiga
gasar su wadda aka tsara farawa a ranar
Jumma'a.
Babban asibitin birnin ya lalace sakamakon
girgizar kasar, inda wasu hotuna da aka nuna a
kafar talbijin din kasar suka nuna yadda ake kula
da marassa lafiya a wajen asibitin.
Biranen Palu da Donggala na dauke da mutane
fiye da dubu 600.
Shugaba Joko Widodo, ya ce an tura sojoji
wuraren da lamarin ya faru domin taimaka wa
jami'an agaji a aikin ceton da suke.
Tuni dai aka rufe babban filin jirgin saman Palu
tun bayan afkuwar girgizar kasar.
Kazalika an tura wasu jirage soji domin kai
kayan agaji ga wuraren da alamarin ya afku daga
Jakarta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: