Wata ambaliya mai karfi ta mamaye yankin Otuoke, mahaifar tsohon Shaugaban Kasa, Goodluck Jonathan a jihar Bayelsa.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa garin Otuake, garin da ke cikin Karamar Hukumar Ogbia, na daya daga cikin garuruwan da ambaliyar ta fi shafa.
Wasu mazauna yankin a yanzu su na amfani da kwale-kwale ne idan za su isa zuwa gidajen su.
Ambaliyar ta faru ne sakamakon malalar da ruwa ya yi daga Kogin Orashi-Taylor da wawakeken gwadaben ruwa na Epiec da ke cikin Kogunan Jihar Rivers da Bayelsa.
NAN ta kara ruwaito cewa idan ba a manta ba, cikin 2012 ma sai da ambaliya ta mamaye garin Otuake, har ruwa ya shiga cikin gidan Jonathan.
Daya daga cikin wadanda ruwan ya yi wa ta’adi, mai suna Solomon Oru, ya roki Gwamnatin Tarayya da Hukumar Agaji Gaggawa, NEMA su kai masu dauki, domin a yanzu ba su da wata hanyar shiga gidajen su sai dai a cikin kwale-kwale kadai.
Ya kara da cewa akasarin kayayyakin su duk ruwa ya lalata su.
Ya kuma ci gaba da cewa ruwan ya kwararo musu macizai wadanda ke kawo musu barazana ga rayuwar su.
Wani mazaunin yankin mai suna Emmanuel Peter, ya ce barayi sun addabe su don haka ba su iya zuwa ko’ina, domin da sun fita za a bi gidajen su ana sace musu dan abin da ya rage musu.
Wakilin NAN da ya ziyarci yankin, ya tabbatar da cewa ambaliya ba ta shafi yankin da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Otuake ba, domin ya ga dalibai na ta kai da kawo a cikin makaranatar.
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da kai ziyarar gani da ido a yankin, ya bayyana ambaliyar da cewa babban bala’i ne. Ya yi alkawarin gwamnatin tarayya za ta taimaka.
Premiumtimeshausa.
0 Comments:
إرسال تعليق