Ina 'yan sanda suka ajiye 'yan Shi'a 400 da suka kama?
LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama 'yan kungiyar 'yan Uwa Musulmi 400 da ake zargi da tayar da yamutsi a Abuja, babban birnin kasar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Mr Jomoh Moshood ya aike wa manema labarai ta kara da cewa an kama mutanen ne dauke da kwalabe 31 na bama-baman da aka hada da fetur da muggan makamai.
A cewar sanarwar ana gudanar da bincike kan 'yan Shi'ar kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.
Mr Moshood ya zargi mabiyan Sheikh Ibrahim El-Zakzakky da kona motocin 'yan sanda da tayar da hargitsi inda ya ce babban sufeton 'yan sandan kasar ya ba da umarni ga 'yan sanda su murkushe 'ya'yan kungiyar a dukkan inda suke a fadin Najeriya.
"An sanya kwamishinonin 'yan sandan jihohin da akwai mabiya kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta El-Zakzakky da su shiga cikin shirin ko-ta-kwana domin murkushe su kamar yarda doka ta tanada sannan su hana 'yan kungiyar tayar da kayar baya a jihohin," in ji sanarwar.
Tun daga karshen makon jiya ne dai mabiya El-Zakzakky suka soma isa Abuja inda za su yi gangami na jimanin mutuwar Hussain, jikan manzon Allah Annabi Muhammad(SAW) wanda ake yi duk shekara.
Kalli hotunan artabun 'yan Shi'a da sojoji a Abuja
Mun kashe 'yan Shi'a — Sojin Nigeria
Sai dai sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun hana su shiga lamarin da ya haddasa arangama tsakaninsu har aka yi asarar rayuka.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ranar Litinin ta ce an kashe mabiya Shi'a uku yayin da sojoji suka jikkata akamakon taho-mu-gamar da aka yi a tsakaninsu.
Sanarwar ta ce 'yan Shi'a sun far wa dakarunta da ke sanya ido a wuraren binciken ababen hawa da ke gadar Kugbo/Karu.
"Mabiya mazahabar wadanda ke da matukar yawa sun kutsa kai ta shingen binciken ababen hawa inda suka turmushe 'yan sanda.
"Daga nan ne 'yan sandan suka janye inda suka shiga cikin sojojin da ke yunkurin dakile harbe-harben da mutanen ke yi," in ji sanarwar.
Ta kara da cewa "lokacin arangamar ne mabiya mazahabar uku suka mutu san nan soji hudu suka jikkata, inda aka tura su asibiti domin karbar magani."
Amma 'yan Shi'a sun ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe mambobinsu 24.
Masu sharhi sun shaida cewa ya kamata gwamnati da mabiya mazhabar Shi'a su sasanta tsakaninsu domin gujewa abin da ka-je-ya-komo.
0 Comments:
إرسال تعليق