Kalli wani katon da aka damke yanayiwa karamar yarinya fyade
An damke wani dan kasar Indiya mai shekaru 34 da haihuwaa a daren jiya yayinda yake yiwa wata yar karamar yarinya fyade cikin motarsa a garin Lusaka, kasar Zambia. Katon ya yaudari yarinyan ne ta hanyar siya mata kaza da dankalin turawa sannan ya shiga da ita cikin motarsa domin tarawa da ita. Amma yayinda mutane suka ga mota na motsi da kanta, sai suka bude motan suka ga kato kan yar karamar yarinyan yana zufa. Bayan damkeshi, yarinyan ta bayyana cewa yunwa take ji lokacin da ya saya mata abinci. An garkameshi a ofishin yan sandan Kabtawa kuma zai gurfana gaban kotu da laifin fyade wa karamar yarinya
0 Comments:
إرسال تعليق