Shugaban Chocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo da Shugaban Roman Catholic Diocese ta Sokoto, Bishop Matthew Hassan Kukah , da sanannen malamin addinin Islama na Kaduna Dr. Gumi sun shiga wata ganawar sirri da tsohon shugaba kasa Olusegun Obasanjo da dan takarar jamiyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar
Ana ganawar sirrin ne a Gidan tsohon Shugaban kasa Chief OLusegun Obasanjo dake Abeokuta.
Dan takarar shugabancin kasa a karkashin PDP Alhaji Atiku Abubakar ya hallara gun taron karfe 1:07pm inhda ya wuce kai tsaye zuwa inda ake tattaunawa a Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), Oke-Mosan.
Ragowar mutanen da suka shiga tattaunawar sun hada da Tsohon Gwamnan Ogun , RIvers Gbenga Daniel da Liyel Imoke , se Senator Ben Bruce among others.
Har yanzu suna cikin tattaunawa yayinda ake hada wannan rahoton.
0 Comments:
إرسال تعليق