Dalilin da yasa na karfafawa Rahama sadau gwiwa wajen bada hakuri
Fitaccen jarumin kuma mai tauraro Ali Nuhu shine kashin bayan kokon bara da jaruma Rahama Sadau tayi na neman gafara bisa ga abun da ya faru a baya wanda yayi sanadiyar korarta daga farfajiyar kannywood.
A rahoton da jaridar Dailytrust ta fitar Ali Nuhu yace jarumar ta bada hakuri bayan ta gane cewa tayi kuskure, yayi ikirari cewa dan Adam ajizi ne wanda baya rabuwa da aikata kuskure.
n mu na manya a masana'antar, ya zama dole mu wayar da kan kananan jarumai na dandalin, shiyasa na karfafa mata gwiwa wajen bada hakuri"
"Yana da kyau idan mutum ya gane kurakuran shi ya bada hakuri.
Rahama tayi kokari da ta bada hakuri kuma ta dau alkawari cewa baza ta kara aikata kuskuren ba.
Ta aika wa kungiyar MOPPAN wasikar neman gafara wanda na san membobin kungiyar suna tattaunawa akai" Inji Ali Nuhu.
Ita dai Rahama Sadau ta fito fili ta baiwa jama'a hakuri bisa ga kuskuren da tayi wanda yasa aka koreta daga dandalin kannywood.
Tayi hakan ne yayin data ziyarci gidan rediyo na Rahama Fm dake jihar Kano cikin wani shiri mai suna "ku karkade kunnuwan ku".
0 Comments:
إرسال تعليق