Fitacen malamin addinin islama dake garin Kaduna Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya yi kira da mahukunta da su tsige gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje bisa zarginsa da karbar rashawa.
Shehin malamin ya yi wannan jawabi ne jiya Alhamis game da kudin rashawa da aka kama gwamna Ganduje yana karba.
Malam ya nuna bambanci dake tsakanin kudin da gwamnoni suke canzawa daga wani aiki zuwa wani aiki da kuma karkatar da dukiyar al'umma da cinye ta da suke yi da bambanci tsakanin wanda zai karbi kudi domin ya bada wata kwangila.
Idan kana kare musulunci ne to ka bi abinda musulunci ya ce, idan kuwa kana kare siyasa ne to ka sani siyasar za ta barka a duniya addini ya raka ka lahirarka.
5 hrs · Facebook for Android · Pub
0 Comments:
إرسال تعليق