[post by samaila umar lameedo]
EFCC ta gargadi 'yan canjin kudi a Najeriya
LABARAI DAGA 24BLOG
Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati Ibrahim Magu ya gargadi masu canji kudi da su daina taimaka wa harkokin cin hanci da rashawa da wadansu 'yan siyasa suke yi a kasar.
Shugaban ya ce hukumar za ta gurfanar da duk wani dan siyasa ko banki da aka samu laifin taka dokokin hada-hadar kudi a kasar, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC.
Me Rabi'u Kwankwaso ya je yi Kano?
El-Rufai ya yi kuskure da ya zabi Musulma mataimakiyarsa
Kun san matar da za ta zama mataimakiyar el-Rufai?
Ya bayyana hakan ne lokacin da shugabannin kungiyar 'yan canjin kudi ta Najeriya (ABCON) suka kai masa ziyara a hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.
Shugaban ya zargi wadansu 'yan siyasa da masu canjin kudi da hadin baki wajen karkatar da kudin gwamnati.
Daga nan ne shugaban kungiyar Alhaji Aminu Gwadabe ya yaba da shugabancin hukumar kuma ya ce wadansu mambobinsu marasa rijista ne suke harkokin da suka saba wa doka.
Har ila yau, ya ba da tabbacin cewa "kimanin mambobin kungiyar ABCON masu rijista 5000 ne suke taimaka wa hukumar EFCC wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar."
Ya kuma ce akwai "kimanin 'yan canji 100,000 wadanda ba su da rijista a Abuja kawai, kuma su ne suke ba ta mana suna.
"Muna bukatar hada karfi da hukumar EFCC wajen yaki da wadannan bata garin
0 Comments:
إرسال تعليق