Fadar shugaban kasa ta hannun me baiwa shugaban kasar shawara akan akan kafafen sadarwa na zamani Lauretta Onochie ta karyata ikirarin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku abubakar da yayi na cewa ya taso a matsayin marayane kuma har tallar itace yayi.
Atiku ya bayyana hakane ranar Litinin a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zaben shi.
Saidai da take mayar da martani akan wannan magana Onochie tace, kada fa 'yan Najeriya su yadda da maganar ta Atiku da yake cewa wai ya taso a matsayin maraya domin duk zugi ta malle ce.
Tace maraya shine wanda mahaifinshi da mahaifiyarshi suka mutu. Ta tunawa mutane da abinda Atikun ya rubuta a littafinshi me suna My Life a shekarar 2013 a shafi na 30 inda yace mahaifiyarshi ta rasu a shekarar 1984. Ta kara da cewa a lokacin Atikun yana da shekaru 38.
Kuma yakai shekarun da zai iya saiwa mahaifiyarshi gida.
Tace, menene amfanin yin irin wannan karyan? dan kawai a yaudari 'yan Najeriya dan samun tausayinsu? tace rashin girmamawane da kuma cin fuska ga 'yan Najeriya ace wani dan takara ya musu karya.
Tace yana tunanin ba zamu iya gano karyar da yayi bane? Tace tabbas zamu iya kuma shugaba Buhari ko mataimakinshi Osinbajo ba zasu taba yiwa 'yan Najeriya karyaba.
0 Comments:
إرسال تعليق