wajan tana kuka Wanda hawaye ne
ke zuba bakajin kara, inna larai tasa
kafa ta hankade ta tafadi kasa, tace
mayya wlh naso kibi uwarki kema
amma duk da haka bata baci ba,
zanta azabtar dake har karshan
rayuwanki a haka zaki zauna, tai
tsaki ta shige daki, ganin haka
fatima tai saurin mikewa duk da
jikinta na ciwo ga yunwa haka ta
nufi sauro don ta kwanta, duk ta
kasa bacci sai tunani take tayi, irin
azabar da inna larai take bata, a
haka bacci barawo ya dauketa, bata
farka ba saida asuba alokacin anata
kiraye kirayen sallah, jikinta ya mata
nauyi sai taji kaman ma da bataji
komai ba haka ta tashi dakyar tai
alwala tai sallah a zaune domin
yanda take jin kanta bazata iya
tsayuwa ba, bayan ta idar, ta dan
kwanta amma ta kasa bacci, sai
tunani takeyi har gari ya fara
wayewa ta mike domin zuwa diban
ruwa a rijiya dakyar take diban
ruwan, tana nishi ga wani zazzabi
da takeji a jikinta, haka ta gama
diba dakyar harta gama ta dauko
wanke wanke, hannunta duk yayi
jaa, kalan na wahalan nan, harta
gama wanke wanken inna larai bata
fito ba, ta dauko tsintsiya tana
shara kaman zata fadi jikinta sai
zafi yake tana ta kyar kyarwa dan
sanyi saida ta gama tana kwashewa
inna larai ta fito, tana yatsina fuska
ta galla mata harara tace uban wa
zai hada murhu da kikaki hadawa
tun dazu, fatima tai saurin cewa
yanxu zan hada, inna larai ta dauki
buta tai bayi tana ta faman bala'i
kaman tana fada da babban mace,
fatima ta hada murhun ta dauko
tukunyan da ake sa ruwan zafin
kunu tasa ruwa, inna larai ta gama
hada kunun ta dauki kayanta takai
daki tace kixo ki daura gyadar, haka
tazo ta daura, tana ta jiran a bata
kunu amma inna larai tai mursisi ta
hanata, kuma tana tsoran magana
taci duka gashi bata jin dadin
jikinta, har gyadan ta nuna, ta
dauko tsinma ta kama tukunyan
aiko tana dauka ya kufce a kasa a
harya zuban mata a kafa, ta kwalla
wani uban ihu da kuka mai karfi ta
kama kafan,domin ruwan gyadan ya
zuban mata a kafa sosai, ga gyadar
ta zube a kasa, inna larai ce ta
karaso wajan da sauri, tana xuwa
tayi turus, wato gyadar kika
zubarmin a kasa aiko Ya'u wlh
sainayi maganinki, kafin inna ta
karasa, har Ladidi makwabciyarsu,m
aman Amina kenan kawar fatima,
tashigo tana fadin fatima lfya ina
bayi naji ihunki, tana karasawa taga
kafanta Wanda ya tashi fatan ta
salibe tace subhanallah, tai sauri ta
dauko wata roba ta dibo ruwa ta
kama kafan tasa mata, aiko inna
larai data tsaya kallonsu tai sauri ta
cire kafan a roban tahau dukan
fatiman tana fadin wato asara
kikamin ki zubarmin da gyada ki
tsaya kina ihu kiki kwashewa, Ladidi
dake gefe tai saurin janye fatima
tana Haba larai, wannan wani irin
rashin imani ne, kina ganin yanda
ruwan zafi ya zube mata a kafa, ji
yanda kafan ta salube amma ki
rufeta da duka, da wanne zataji,
inna larai tace an daka din ina
ruwanki shin maima ya kawoki
gidan nan maza kifitar min a gida
munafika kawai, Ladidi tace zan fita
amma larai komai kikeyi ki dinga jin
tsoran Allah domin hakkin yarin
yannan wlh bazai barki ba, kuma
nan gaba sai kinyi dana Sani,ta
kama hanya ta fita, aiko Inna Larai
taita ban bamin bala'i, ta kama
fatima tai mata likis sannan tasata
kwashe gyadar, haka ta dauka ga
yunwa ga ciwo a kafanta ga jiri
tanaji haka tai bakin titi, dakyar ta
karasa tana Isa ta fara asiya gyada
muryanta baya fita da kyau, wata
mota ta hango ta tsaya alaman
wanine zai sauna aiko da sauri ta
nufi wajan amma kafinta karasa ji
kake keeeeeeeeeeeeee, da kara mai
karfi aiko nan danan tai kasa
sumamma ga jini nata gudara a
wajan, nan da nan mutane sukayi
kanta yayinda mai motan yai fakin a
gefe ya fito, a rude yana fadin
innalillahi'wa inna ilaihira jiun,
Malam Usman daya sauka a mota
shima yai saurin karasawa yana
lekawa,turus ya tsaya don ganin
fuskan wanda take kwance,
mutumin daya bigeta yana ta waya
Santa muje mu kaita asibiti,Malam
Usman yai saurin karasawa yana
fadin muje Malam, nine mahaifinta,
Wanda yana maganan ne a rude
nan da nan suka shiga suka dau
hanya don zuwa asibiti fatima zarah
ko[truncated * numfashi ba ta yi.
Wani asibiti suga gani a hanya nan
danan suka Shiga da sauri akayi
emergency da ita domin ceto
rayuwarta, likita ya shiga shi da
wasu nurses guda uku, malam
Usman dai kasa cewa komai yayi
sai hawaye dake silalo mishi daka
ido, Wanda duk maganan mutanan
kauyen ya fara dawowa kunnenshi,
akan irin azaban da larai take bata,
tabbas ya kamata ace ya yarda
amma ya rasa dallin da yasa baya
son laifin larai, nan da nan yaji wani
tsanarta a ranshi, tabbas komai ya
faru da fatima Zarah, larai ce kuma
bazai barta ba, dafashi din da akayi
yasa ya dawo daka tunanin da
yakeyi,mutumin da ya bige fatima
yace dan Allah Malam kayi hakuri
wlh na rasa yanda akai abun ya
faru, duk kokarin in taka birki amma
na kasa, Wlh ina cikin tashin
hankali na fito ko driver dina ban
jiraba, saboda a firgice nake, da na
Allah yama rasuwa, malam Usman
ne yace Allah sarki, Allah ya gafarta
mai, ai Alhaji tafiya ya kamata kayi,
don samun jana'izan shi, Alhajin da
mamaki yake kallon Malam Usman,
domin baiyi zaton hakan zaice ba
yace aiya kamata in San halin da
yarinyan ke ciki,Malam Usman yace
ba komai kaje kawai, mutumin yayi
gdy tare da ciro kudin da baisan ko
nawa bane yace gashi ka rige,xanje
in biya asibitin suma, sannan yace
ma Malam Usman zai dawo ya duba
jikin nata, kai tsaye reception suka
nufa, ya samu receptionist ya bata
kudi yace in bai isaba ga katin
shinan ta kira ta fada masa Kafin ya
dawo, ta amsa sannan ya amsa no
din doctor din ya fito, tare da ma
Malam Usman sallama da alkawarin
zai dawo, bayan ya tafi ne Malam
Usman ya dawo asibitin duk a rude
yake yana jiran yaji mai za'ace
masa domin ya kwashe wajan minti
talatin baiji likita ya fitoba, nan da
nan ya fara tunanin abunda ya faru
a baya.... . Tuna baya.... Garin
kaduna a cikin wani kauye
fanbeguwa yayi sanyi saboda lokaci
ne na sanyi yayin da duk Wanda ka
ganshi yana sanye da rigan sanyi,
wasu kuma kalan rigan leda dinnan
suke sanye dashi, gidan Malam
tanimu gidane na kasa matanshi
biyu Hajara, da karima, Hajara itace
uwar gida tana da yara biyu duka
mata, jamila da suwaiba, sannan
karima itace Amarya danta daya
Usman saida ta dauki tsawon lokaci
kafin ta haihu ganin ta haifi namiji
Malam tanimu ya dauki son duniya
ya daura wa Yaron, Wanda shine
sanadin rashin jituwansu,
tsakaninta da abokiyan
zamanta,haka rayuwa taci gaban
musu Usman indai ya fito tsakan
gidan to yashiga uku,domin Hajara
ta koya ma yan uwanshi tsananshi,
alokacin ba'a dauki karatun boko da
mahimmanci ba, Usman ya samu
ilimin addini dai2 gwar gwado,
yayinda yan uwanshi mata suka
kaurace ma islamiyan basa zuwa
Malam tanimu yayi fadan har ya gaji
ya zuba musu ido, a haka suka
sami mazajen aure sukayi, shi
kuma Usman yaci gaba da kula da
aikin gonan mahaifin nashi, in an
Nome ya kai kasuwa ya siyar haka
yakeyi, mahaifinshi na alfahari
dashi sosai, a kasuwan da yake kai
kaya ya hadu da Hafsat, Wanda
suka kulla soyayya mai zurfi har
magana tayi karfi, ita Hafsat
iyayenta suna u/Bawa cikin
saminaka itama ta kanzo kasuwan
sarin gyada, a haka suka hadu
domin kasuwan babban kasuwa ne
har daka wasu garu ruwa, ana zuwa
haka, dai magana tayi zurfi, aka kai
komai na aure, Malam tanimu ya
bashi wani daki daya da filin dake
wajan yace ya bashi halak malak ko
bayan ranshi, aiko a nan Hajara ta
ke kashe tace Sam bata yarda ba,
domin ana nunawa yayanta
banbanci, suma sai an basu, Malam
tanimu yace Hajara Yaron nan duk
abunda na bashi bai kamata kiyi
bakin ciki ba domin shine Wanda
yake taimaka min, ni...................
0 Comments:
إرسال تعليق