Zargin cin hanci: Ganduje ya hallarci daurin aure a maimakon amsa gayyatar majalisa
LABARAI DAGA 24BLOG
- Kwamitin bincike kan zargin karbar cin hanci da ake yiwa gwamna Ganduje na jihar Kano ta gayyaci gwamnan a yau
- Sai dai gwamna Dr Abdullahi Ganduje bai samu damar amsa gayyatar da kansa ba inda ya aike da wakili
- Daga bisani an gano ashe gwamnar ya tafi wajen taron daurin aure ne a maimakon amsa gayyatar kwamitin
A yau, Juma'a 2 ga watan Nuwamba ne Kwamitin bincike da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa ta gayyaci gwamna Dr. Abdullahi Ganduje na jihar ya bayyana a gaban domin kare kansa daga zargin karbar cin hanci da rashawa da ake masa.
Sai dai gwamna Ganduje bai samu damar bayyana gaban majalisar da kansa ba inda ya tura kwamishinan yada labarai na jihar Kano domin ya wakilce shi amma hakan bai yiwa majalisar da di ba.
Ganduje ya tafi daurin aure maimakon amsa gayyatar kwamitin majalisa
Rahotani da muka samu daga Arewa 24 ya bayyana cewar an gano gwamna Ganduje ya hallarci daurin auren giyar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata a maimakon amsa gayyatar majalisar.
Legit.ng Hausa ta gano cewar an daura auren ne a unguwar Fagge da ke cikin garin Kano.
Galibin al'umma da suka tofa albarkacin bakinsu kan lamarin sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda gwamnan ya ki amsa gayyatar majalisar da kansa duk da cewa wata muhimmiyar aiki bane ya shige masa gaba.
Wakilin gwamnan ya shaidawa kwamitin binciken cewar faye-fayen bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa da ke nuna Ganduje na karbar wasu daloli ba komi bane illa sharri irin na 'yan adawa da ke kokarin kawo cikas ga gwamnan.
0 Comments:
إرسال تعليق