[post by samaila umar lameedo]
INEC za ta kammala baje kolin sunayen masu zabe
LABARAI DAGA 24BLOG
A ranar Litinin 12 ga watan Nuwamba ne hukumar zabe a Najeriya za ta kammala aikin baje-kolin sunayen masu jefa kuri'a na tsawon mako guda a cibiyoyin zabe da ke fadin kasar.
A ranar Talata 6 ga watan Nuwamba ne hukumar ta kaddamar da aikin baje sunayen, don ba wa mutanen da suka yi rijista damar yin gyare-gyare da korafi da ankaraswa da rai-raye wadanda ba su cancanci kada kuri'a a zaben 2019 ba.
Mai magana da yawun hukumar Malam Aliyu Bello, ya shaida wa BBC cewa, aikin baje kolin sunayen masu jefa kuri'ar da aka yi na tsawon mako guda ya samu gagarumar nasara, kuma ga dukkan alamu zai yi tagomashi da armashi wajen gyara rijistar da za a yi zabe da ita a 2019.
APC ta ce INEC ba ta iya dakatar da 'yan takararta a Zamfara
'Yan takara 78 ne za su kalubalanci Buhari
Zaben 2019 sai ya fi na 2015 nagarta — INEC
Malam Aliyu Bello, ya ce duk wanda bai je ya duba sunansa ba, to shi ya yi sake, domin hukumarsu ta ba wa kowa dama a kan ya je ya duba sunansa.
Ya ce, mafi yawancin wadanda suka cancanci kada kuri'a a kasar sun je sun duba sunayesnu.
Dangane da batun ko za a kara wa'adin baje kolin sunayen masu zaben, ya ce ya zuwa yanzu dai ba a ambata hakan ba domin da zarar wa'adin da aka diba na baje kolin sunayen ya cika, to da yiwuwar hukumar zabe ba za ta sake wani karin wa'adi ba.
To sai dai kuma, wasu mutane sun shaida wa BBC cewa ba su iya ganin sunayensu a rijistar da hukumar INEC din ta kafe
0 Comments:
إرسال تعليق