[post by samaila umar lameedo]
Rikici ya kaure a jam'iyyar PRP a jihar Kano
LABARAI DAGA 24BLOG
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, rikicin shugabanci ya kaure tsakanin wasu `yan jam`iyyar PRP da ke ikirarin cewa su ne `ya`yanta na asali, da kuma wasu da suke yi wa kallon baki, wadanda suke zargin sun yi babakere a jagorancin jam`iyyar.
Masu ikirarin cewa su ne `yan asalin jam'iyyar, na zargin cewa sabbin shiga jam`iyyar sun saba wa akidar PRP da manufofinta na jibantar talakawa, sun juya tsarin jari-hujja, don haka ba za su saurara musu ba.
`Y an jam`iyyar PRPn, wadanda ke ikirarin cewa `yan na-gada ne tun iyaye da kakanni sun yi zargin cewa jam`iyyar na fama da mamayar wasu da suka bayyana da `yan boko, wadanda suka yi mata shigar rana-tsaka suna kokarin wargaza ta.
Dalilin raba garina da Shekarau a siyasa — Takai
'Yan sanda za su fara daure 'yan siyasa a Kano
APC ta kafa kwamitin sauraran kararrakin zabe
Mallam Mukhtar Tanko Zango wanda ke ikirarin cewa shi ne gangariyar shugaban jam`iyyar PRP na jihar Kano, amma shigar wasu jam`iyyar ta sa an yi watsi da shugabancinta, an kuma dora jam`iyyar a kan tafarkin da ya yi hannun -riga da wanda magabata suka assasa ta a kai.
To sai dai kuma bangaren da ake yi wa kallon sabbin-shiga ne a jam`iyyar PRPn, wadanda su ma suka ce su ne ke rike da shugabancin jam`iyyar, wadanda hedikwatar jam`iyyar da kuma hukumar zabe duka sun san da zaman su, sun yi zargin cewa abokan hamayyar cikin gida ne ke zuga masu jayayya da su don cimma wata manufa ta siyasa, ganin jam`iyyar na samun tagomashi.
A jihar Kano dai jam`iyyar PRP ta kwashe lokaci mai tsawo tana zaune lafiya da `ya`yanta.
Ba a fara jin kansu ba sai bayan zabukan fid da gwanin da aka yi a jihar, inda wasu manyan `yan siyasa suka yi kaura daga jam`iyyunsu na asali zuwa jam`iyyar PRP bayan sun nemi takara ba su samu yadda suke so ba.
Jam`iyyar PRP da takwararta ta PDP dai su ne manyan jam`iyyun hamayya a jihar Kano.
Kuma yayin da PDP ta jima tana fama da nata rikicin shugabanci, kasancewar wata maganar ma na kotu, PRP za a iya cewa watakila wutar da ke neman cinye ta ba ta wuce a taru a kashe ta ba duk da cewa ita ma jam`iyyar APC mai mulki na da irin nata matsaloli ko larurar.
Masana kimiyyar siyasa dai na cewa idan jam`iyyun hamayyar ba su gaggauta dai-dai ta gidajennsu ba, to, watakila APC za ta samu damar rawar-gaban-hantsi a babban zaben da ke tafe.
0 Comments:
إرسال تعليق