الجمعة، 30 نوفمبر 2018




Waadin barayin shanun zamfara yacika

Home Waadin barayin shanun zamfara yacika

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Yan sandan Najeriya sun ce sun kashe 'yan ta'adda 104 a jihar Zamfara bayan wata fafatawa da suka yi a karamar hukumar Birnin Magaji, sannan kuma suka lalata maboyar 'yan fashin da dama.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar ta ce jami'an tsaron sun kuma rusa sansanoni uku na barayin, sannan suka kwato shanu sama da 500 da wasu dabbobi da dama.

Rundunar 'yan sandan ta ce an kashe dan sandanta daya yayin kwantar baunar da aka yi musu, sai dai wasu majiyoyin gwamnatin jihar sun shaida wa BBC cewa an kashe 'yan sanda da dama.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin Alhamis din nan, yayin da jami'an 'yan sanda na musamman ke sintiri a cikin dazuzzukan jihar ta Zamfara domin zakulo barayin shanu da masu garkuwa da mutane dake addabar sassan jihar da dama.

    Kotu ta daure shugaban UBE a Zamfara shekara 41
    Buhari ya ce da gangan APC ta tauye hakkin masu son yin takara

Haka kuma dakarun na musamman sun kama sama da mutum 85 da ake zargin gungun masu aikata miyagun laifuka ne a jihar.

Sanarwar ta ce an kuma kwato bindigogi kusan 80 da kuma wasu muggan makamai.

Sakamakon kwanton baunar dai rundunar 'yan sandan kasar ta tura babban mataimakin sufeto janar domin zama babban kwamandan dakarun na musamman.

Babban aikin kwamandan shi ne maido da zaman lafiya a duka fadin Zamfara.
Karin bayani game da Zamfara:

    Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
    Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
    Take: Noma tushen arzikinmu
    Yawancin mutanen jihar manoma ne

#bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: