الأحد، 18 نوفمبر 2018




YADDA AKA KUBUTAR DA TAGWAYEN ZAMFARA

Home YADDA AKA KUBUTAR DA TAGWAYEN ZAMFARA

غير معرف

Ku Tura A Social Media

*Rahotanni daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriay sun baiyana nasarar karbo tagwayen nan mata wadanda barayin mutane su ka sace su, kuma su ka yi kememe su ka ki sako su sai da a ka ba su kudin fansa.*
*Tagwayen nan masu shekaru 16 dama na shirin yin aure ne a watan gobe inda a ka samu wannan akasi kuma cikin ikon Allah bayan barazanar kashe daya daga cikin su, su ka samu kubuta daga hannun miyagun mutanen.*
*Zuwa yanzu dai ba labarin nasarar sako ‘yar uwar tagwayen mai suna Sumayya daga hannun masu satar mutanen. Bayanin da ba mu tantance ba shine kudin fansar da a ka bayar Naira miliyan 15 ne da a ka tara ta hanyar karo-karo.*

Share this


Author: verified_user

0 Comments: