Wasu mata 'yan Najeriya da suka tsinci kansu a Jamhuriyar Nijar bayan sun bar gida da zummar tafiya kasar Saudiyya sun koka kan irin halin ha'u'la'in da suka samu kansu a ciki.
Matan dai na yawon neman ayyukan cikin gidaje kamar wanki da shara da sauransu, ba tare da an biya su hakkinsu yadda ya kamata ba.
WakiliyarmuTchima Illa Issoufou ta ziyarci daya daga cikin matan Zainab a gidan da take aiki, wacce ta shaida mata cewa ta bar Najeriya ne zuwa Nijar da zummar za a kai su aiki Saudiyya, amma kuma a yanzu ba su ga tsuntsu, ba su ga tarko.
"Na farko dai an kawo mu wajen da aka ce ta nan ake tafiya Saudiyya, sai kuma daga bisani aka ce mana an rufe, mu tafi idan an samu lokaci za a daidaita komai.
"Daga baya kuma aka ce ba za a daidaita ba, kowa ya je ya samu gidan aiki don rufawa kai asiri," in ji Zainab.
'Mun sha bakar wahala'
Zainab ta shaida wa BBC cewa a sakamakon rashin tudun dafawa a kasar da ba tasu ba, ya sa suka shiga gararambar neman aiki ba dare ba rana don tallafawa kansu.
"Mun sha wahala sosai domin kafin na samu gidan da nake aiki yanzu, unguwa daidai ne ban sani ba a Yamai, wata unguwar ma idan muka je sai mu bata.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata daga sassan duniya daban-daban na son zuwa Saudiyya ci rani don neman rufin asiri
"Kuma duk yawon neman abin da za mu taimaki kanmu muke, amma a hakan ma ba biyan bukata yadda muke so. Wata ma sai ka gama yi mata aiki sai ta baka abin da bai fi naira 100 ba. Wallahi har kuka muke yi."
Asara
"Ni dai ban shirya komawa gida ba a yanzu tsakani da Allah, saboda ba zan koma na ga takaici ba sakamakon sayar da duk abin da na mallaka don na yi wannan tafiya," a cewar Zainab.
Ta ci gaba da cewa a don haka ne ta dage neman na kanta a Nijar duk da ba ta samu zuwa Saudiyyan ba, inda aka lasa mata zuma a baki cewar za ta mayar da abin da ta kashe a kankanin lokaci.
"Don haka gara na zauna a nan da wuya da dadi har na hada dan wani abin kirki."Mata na tafiye-tafiye zuwa Saudiyya da wasu manyan kasashen duniya ne don neman karuwar arziki a can.
Sai dai da yawansu ba sa iya cimma wannan burin nasu, inda da dama daga cikinsu suke bigewa da karuwanci da mu'ammali da miyagun kwayoyi da kuma barace-barace.
#bbchausa
0 Comments:
إرسال تعليق