Za a hukunta wadanda ake zargi da kisan Janar Alkali
LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar 'yan sanda a jihar Plateau da ke Najeriya, ta ce ta kama wasu mutum 19 da ake zargi da hannu a kisan Manjo Janar Alkali mai ritaya.
A wajen wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar a Plateau a ranar Lahadin da ta wuce, jami'in hulda da jama'a na rundunar DSP Tyopev Matthias Terna, ya bayyana cewa sakamakon binciken da aka gudanar a kan wadanda ke da hannu a kisan marigayin, yanzu rundunar ta kama mutunen da ake zargin.
Dama dai tun a watan da ya gabata sojoji sun mika wa rundunar 'yan sandan mutum 13 da ake zargi da hannu a kisan sojan domin gudanar da bincike a kansu.
Bayan zurfafa bincike ne rundunar ta tabbatar da karin wasu mutum takwas da ake nema ruwa a jallo a kan zargin kisan.
An yi jana'izar Janar Idris Alkali a Abuja
Sojin Najeriya sun kaddamar da yaki da laifi a intanet
An yi sabon kwaroron roba don sojoji
Mutanen da sojojin suka mikawa rundunar 'yan sandan su 13 da kuma wadanda rundunar ta kama da kanta da ma wadanda ta ke nema ruwa a jallo sun hadar da wanda ke da masaniya a kan lamarin, da wanda sua ga yadda aka yi kisan da wadanda suka san wadanda suka yi kisan amma suka yi shiru.
Sauran sun hadar da wadanda aka kama su sakamakon mallakar makamai ciki har da bindiga, da kuma wata mace guda a cikinsu mazauniyar kauyen da abin ya faru ce, kuma tana daya daga cikin matan da suka hakikance cewa ba za a duba ko haka rijiyar da aka gano gawar Janar Alkali ba.
Har yanzu dai ana ci gaba da kokarin gano sauran mutum biyun da ake zargi da hannu a kisan Janar din.
A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kama mutum 30 a yankin Doi Du na jihar Filato a kokarinta na neman Manjo Janar IM Alkali, wanda ya bace tun watan da ya gabata.
Tun a watan Satumba ne iyalan Janar Alkali suka sanar da labarin bacewarsa, inda suka ce ya bar gidansa da ke Abuja a ranar 3 ga watan don zuwa Bauchi inda yake da gona, amma tun daga sannan ba a ji duriyarsa ba, kuma wayoyinsa ba sa tafiya.
Ana zargin cewa an sace Janar Alkali ne wanda yake yin bulaguron a motarsa.
A ranar 29 ga watan Satumba ne kuma rundunar cika aiki da babban hafsan sojin kasa ta Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya kafa don neman Janar Alkali, ta gano motarsa a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na karamar hukumar Jos Ta Kudu.
An yi jana'izar Janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Asabar din da ta wuce.
Mutane da dama ne ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Yusuf Buratai, suka halarci jana'izar Janar din.
Wane ne Janar Alkali?
Dan asalin jihar Yobe ne
Ya shafe shekara 35 yana aikin soja
Ya yi ritaya a watan Yunin 2018
Shi ne babban jami'in gudanarwa na rundunar sojin Najeriya kafin ya yi ritaya
0 Comments:
إرسال تعليق