الاثنين، 19 نوفمبر 2018




Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari

Home Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari

غير معرف

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]
Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari

LABARAI DAGA 24BLOG
Ranar Lahadi ne aka buga kugen siyasa a Najeriya inda 'yan takara a matakin tarayya za su soma yakin neman zaben 2019 gadan-gadan.
Dokokin hukumar zaben kasar, INEC, sun nuna cewa 18 ga watan Nuwamba 2018 ita ce ranar da a hukumance za a soma yakin neman zaben.
Fiye da mutum 30 ne ke takarar shugaban Najeriya, sai dai masana na ganin fafatawar za ta fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP. Dukansu biyu shekarunsu na haihuwa sun wuce 70.
Shugaba Buhari ya ce zai nemi wa'adi na biyu na shugabancin  kasar ne saboda "na kammala ayyukan da na soma."
Shugaban, wanda ya kayar da Shugaba na wancan Goodluck Jonathan a zaben 2015, ya gina takararsa ne kan abubuwa uku: wanzar da tsaro,  samar da ayyuka da kyautata tattalin arzikin kasar, da kuma yakar rashawa
Masana harkokin tsaro da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro - musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.
Ko taron dangin PDP zai iya kada Buhari?
Mene ne dalilin hana Atiku shiga Amurka?
Me ya sa Atiku da Buhari 'suka raba kan 'yan Kannywood'?
Tarihin Atiku Abubakar a takaice
Shekararsa 72
Ya zama gwamnan jihar Adamawa
Ya yi mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
Hamshakin dan kasuwa ne
Ya rike mukami a hukumar Customs
Ya sha fuskantar zarge-zargen cinhanci da rashawa
Musulmi ne daga arewacin Najeriya
Sai dai sun nuna gazawar shugaban wajen shawo kan matsalolin masu satar mutane don karbar kudin fansa da rikicin namona da makiyaya - wadanda suka yi kamari a shekarun baya bayan nan.
Kazalika an sha caccakar Shugaba Buhari saboda gaza yin tagomashi kan inganta tattalin arzikin Najeriya, ko da yake gwamnatinsa ta sha cewa zai dauki lokaci kafin kasar ta warke daga masassarar tattalin arzikin da ta fada a ciki lokacin da ta karbi mulki, kamar yadda ministar kudi Zainab Ahmed ta jaddada a hirar ta da BBC a makon jiya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: