[post by samaila umar lameedo]
Zan yi maganin Democrats - Trump
LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi imanin zai iya aiki tare da 'yan jam'iyyar Democrats bayan sun samu rinjaye a majalisar wakilai a zaben rabin wa'adi da aka gudanar.
A wani zazzafan taron manema labarai da aka shafe lokaci Trump na amsa tambayoyi, ya ce yana ganin za a fahimci juna ta fannin ayyuka da kasuwanci da kiwon lafiya tsakaninshi da 'yan Democrats.
Sai dai ya yi gargadi ga 'yan majalisar jam'iyyar cewa yana da makamin da zai yake su ga duk wani yunkuri na binciken gwamnatinsa.
Ya ce duk 'yan jam'iyyar Democrats suka yi yunkurin bincikensa to yana da majalisar dattawa da jam'iyyarsa ta Republican ke da rinjaye.
"Idan sun shirya yin wasa, mun fi su iyawa, Saboda muna da abin da ake kira Majalisar dattawa."
Duk da Trump ya ce yana iya aiki da Democrats a majalisar wakilai, amma ya yi barazanar cewa zai fara gudanar da bincike kan jam'iyyar idan har ta bincike shi kan batun tsarin harajinsa.
Sai dai dan majalisar Democrat Gregory Meeks ya ce Trump ba zai iya amfani da su ba.
Ya ce dama sun yi hasashen za su samu rinjaye a majaliar wakilai, kuma abin da suka yi ke nan. "Don haka dole yanzu musa ido ga wannan shugaban don kada ya dinga abin da ya ga dama."
Shugaba Trump dai ya yi ikirarin cewa zaben rabin wa'adin wata babbar nasara ce gare shi duk da kuwa ya sha kaye a majalisar wakilai.
0 Comments:
إرسال تعليق