An yi wata kyakkyawar budurwa da ke zaune a daya daga cikin jihohin Arewa mai suna Salma (ba sunanta na gaskiya ba). Salma ta kasnace yarinya ce mai natsuwa da yin biyayya ga iyayenta daidai gwargwado. Sunan mahaifinta Alhaji Balarabe yayin da mahaifiyarta kuma Hajiya Maryam. Alhaji Balarabe mutum ne mai dukiya daidai gwargwado, domin hamsakin dan kasuwa ne. Ya yi karatun zamani, amma bai taba yin aikin gwamnati ba, sai ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci. Kafin kankanen lokaci Allah Ya azurta shi, inda ya mallaki kadarori masu yawa da suka hada da manyan shaguna da gidaje da motocin dakon kaya da na sufuri da kuma motocin shiga. Ya dauki ma’aikata da dama da ke cin abinci a karkashinsa.
Mutum ne mai son taimakon al’umma, don haka jama’a ke tururuwa zuwa gidansa don neman taimako. Kuma daidai gwargwado yakan taimaka wa al’umma, hakan ta sa jama’a ke yawan yi masa addu’a da fatan alheri.
Alhaji Balarabe ya dade bai samu haihuwa ba, ya kwashe shekaru masu yawa kafin ya samu haihuwar ’ya da ya sanya mata suna Salma.
Iyayen Salma sun nuna mata gata wajen sanya ta a makaranta har ta yi karatun jami’a.
Salma ta shaku da mahaifinta Alhaji Balarabe, don haka ba ta boye masa komai, duk abin da ya shige mata duhu takan same shi don ya ba ta shawarar da ta dace ko ya dora ta a kan hanya. Hasali ma yadda Salma ta shaku da mahaifinta Alhaji Balarabe, ba ta shaku da mahaifiyarta Hajiya Maryam ba.
Salma ba ta taba bata wa mahaifinta rai a kan wani abu ba, saboda irin biyayyar da take yi masa. Hasali ma Alhaji Balarabe yakan yi alfahari da irin biyayyar da ’yarsa Salma take yi masa, inda a kullum yake yi mata addu’a da kuma fatan alheri.
Mu kwana nan
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883
0 Comments:
إرسال تعليق