An kashe akalla mutum 15 a Zamfara
Wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 15 a kauyen
Magamin Diddi cikin yankin karamar Hukumar Muradun ta
jihar Zamfara.
Bayanai sun ce 'yan bindigar sun auka kauyen ne bayan sallar
azahar ranar Asabar, inda suka rika harbi kan mai tsautsayi.
Zuwa yanzu jami'an tsaro ko hukumomin jihar ba su ce komai
game da wannan al'amari ba
Wani mutumin yankin ya ce mutanen kauyen da dama ne suka
jikkata sakamakon harbe-harben da barayin suka yi tsawon
lokaci ba tare da samun dauki daga jami'an tsaro ba.
Jihar Zamfara tana fama da hare-haren 'yan fashin shanu da
masu satar mutane don neman fansa, wadanda suka
tagayyara yanki.
Shaidan da BBC ta zanta da shi ya ce an kashe dansa na
cikinsa da kuma jikansa a lokacin wannan hari.
"Akwai Iroro, wanda yake jikana ne sun harbe shi kuma bayan
ya fadi suka bi shi suka yi masa yankan rago.
Shi ma yana tare
da abokinsa. Akwai wani Dan Yaya shi ko tafiya ma ba ya iya yi
don ya samu matsala, amma sai da suka harbe shi. Shi kuma
yarona yana gudu, suka taras da shi suka harbe," in ji shi.
Ya ce akwai 'yan gida daya, su hudu da aka harba, amma dai
yana jin biyu suna nan ba su mutu ba.
A cewarsa sun tuntubi hukumomi don su kai wa 'yan garin
dauki, amma dai har maharan suka gama abin da suka yi babu
wani jami'in tsaro da ya je.
Shaidan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ranar
Juma'a 'yan sa-kai sun je wani kauye a yankinsu inda irin
wadannan barayi ke samun mafaka.
Inda suka je masallaci, suka samu wasu mutane da suke
zargin barayi ne su uku suka kama, suka taho da su nan garin
Magami, inda suka tsare su kafin jami'an tsaro su je su tafi da
su.
Don haka, mutane na ganin wannan mai yiwuwa shi ya harzuka
'yan fashin, suka yiwo shiri suka kai musu harin ranar Asabar,
in ji shi.
Jami'an tsaron da ke zaune a karamar hukumar Muradun sun
yi nisa matuka da kauyensu wanda ba shi da kwalta.
Kafin a kai musu dauki gaskiya sai an dau lokaci tun da a
bakin daji suke.
BBC ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, sai dai
jami'in da ke magana da yawun 'yan sandan bai amsa kiran da
aka yi ta yi masa ba.
0 Comments:
إرسال تعليق