Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Iran Admiral Habibullah Seyari ya ce ba za su taba bayar da izini ga jirgin ruwan Amurka samfurin USS John C. Stennis da ke daukar jiragen sama na yaki ya wuce ta gabarsu ba.
A yayin wani bikin yaba wa sojojin Iran da aka gudanar a Jami’ar Dafus ta Soji, Admiral Seyari wanfa ya amsa tambayoyin manema labarai ya ce, “A baya ba a taba ganin irin wannan jirgi a gabar tekun Basra ba, amma akwai wasu nau’uka daban-daban. Ba za mu taba bayar da izini USS John C. Stennis ya zo kan iyakarmu ba.
Sannan don nuna adawa ga jirgin na Amurka, Iran ta gudanar da wani atisaye a tekun Basra.
Source. Jaridar Aminiya
0 Comments:
إرسال تعليق