- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kira kan zaben shugabannin na gari a zaben 2019
- Obsanjo ya shawarci al'ummar Najeriya kan tabbatar da bunkasar ci gaban kasa ta hanyar amfani da kuri'un su a matsayin makamai
- Obasanjo ya ce ba bu wani dan takara ko wata jam'iyya da za ya yiwa yakin neman zabe
Mun samu cewa, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya kirayi al'ummar kasar nan kan yiwa kawunan su karatun ta nutsu gami da amfani da idanun basira da kuma hangen nesa wajen jefa kuri'un su ga 'yan takara a yayin babban zabe na 2019.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasar yayin shawartar al'ummar kasar dangane da zabin da ya kamatun su yi a zaben badi, ya kuma bayyana cewa ba bu wani dan takara da za ya yiwa yakin neman zabe.
Majiyar Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Obasanjo ya bayyana hakan ne cikin jawaban da gabatar yayin halartar taron kasa na Sarakunan Gargajiya 'yan kabilar Yarbawa al'ummar Owu karo na 27 da aka gudanar a garin Iwo na jihar Osun.
Ba bu wanda zan yiwa yakin neman zabe - Obasanjo
Ba bu wanda zan yiwa yakin neman zabe - Obasanjo
Obasanjo cikin jawanbansa tare da bayar da shawarwari, ya ce dole al'ummar Najeriya su tabbatar da zabin shugabanni masu kishin kasa a zukatansu domin ingantawa da kuma bunkasar ci gaban ta da habaka.
Ya ci gaba da cewa, bunkasa da kuma ci gaban kasar nan na da babbar nasaba ga jagorori na gari da sai al'ummar Najeriya sun tashi tsaye wurjanjan ta hanyar yiwa kawunan su karatun ta nutsu da kuma hangen nesa yayin zaben kasa na badi.
0 Comments:
إرسال تعليق