الأربعاء، 5 ديسمبر 2018




City ta ci gaba da kankane teburin Premier

Home City ta ci gaba da kankane teburin Premier

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Manchester City ta je ta doke Watford 2-1 a wasan mako na 15 a gasar Premier da suka kara a ranar Talata.


City ta ci kwallo ta hannun Sane da Mahrez, yayin da Watford ta zare daya ta hannun Doucouré saura minti biyar a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon City tana nan a matsayinta na daya a kan teburin da maki 42, kuma har yanzu ba a doke ta ba, inda ta ci karawa 13 da canjaras biyu.

Ita kuwa Watford tana ta 11 da maki 20, wadda ta ci wasa shida da canjaras uku aka doke ta sau shida a wasannin Premier ta bana.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga.
Bournemouth 2 - 1 Huddersfield
Brighton 3 - 1 Crystal Palace
West Ham 3 -1 Cardiff City
BBChausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: