الثلاثاء، 4 ديسمبر 2018




Jami'yyun siyasar Najeriya sun yi wa INEC raddi kan kudinda za a kashe na kamfen

Home Jami'yyun siyasar Najeriya sun yi wa INEC raddi kan kudinda za a kashe na kamfen

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ce za ta yi amfani da wasu hanyoyi domin bin diddigin kudaden da jam'iyyun siyasa ke kashewa, a lokacin yakin neman zabe.

Al'amari da ya dade ana ka-ce-na-ce akansa, idan aka dubi irin makudan kudaden da jam'iyyu ke kashewa a lokutan zabe.

Tuni dai manyan jam'iyyun siyasar kasar suka soma tsokaci a kan matakin

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta ce matakin ya bata mamaki ko da yake Alhaji Yahaya Ability wanda jigo a jamiyyar PDP a jihar Niger ya yi kira a kan ta tabbatar ta yi adalci.

"Jam'iyyarmu ina ta ga kudi, bamu da gwamnati saboda haka nan gwargwadon abinda mu ke kasuwanci shi ne mu ka ga ya dace mu tattara mu zo mu tafi zabe" in ji shi.

Ita kuwa jam'iyyar APC mai mulki ta ce matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi dai- dai saboda a cewarta wannan shi ne zan banbance tsaki da tsakuwa. Hon Faruk Adamu Aliyu Birnin Kudu, jigo a jamiyyar APC mai mulki ya ce matakin zai sa a gane wadanda suke kokarin kwatantawa da kuma wadanda suka rika almundahana da kudin mutane .

"Ina son na tabbatar da cewa a yanzu da nake magana ba bu wani naira daya da ta cikin jami'yyar APC wadda ba karbar aka yi daga hannun yan jami'yya ba". Misali kwanan aka sayar da fom-fom na tsayawa takara wadanda mutane da yawa sun yi karaji akai, don me yasa ya yi tsada.

Sai dai wasu masu sharhi a kasar sun nuna shaku akn ko hukumar zaben za ta iya wannan aiki na sa ido kan makudaden kudaden da jam'iyyu suke kashewa a lokutan zabe, saboda a cewarsu baya ta sha korafin cewa ayuika sun mata yawa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: