الأحد، 9 ديسمبر 2018




Kaine La'ananne Ba Mu Ba- Cewar Nura Hussain ya mayarwa Dr, Ahmad Gumi martani

Home Kaine La'ananne Ba Mu Ba- Cewar Nura Hussain ya mayarwa Dr, Ahmad Gumi martani

غير معرف

Ku Tura A Social Media
tw
Wani faifan bidiyo da ya fito na
tauraron fina-finan Hausa, Nura
Hussain inda ya saka wani

wa'azin malamin addinin
Muslunci Sheikh Dr. Ahmad Gumi
ya caccaki shugaban kasa, Buhari da ma masu goyon
bayanshi. Anji malamin yana cewa yanzu
dai shekara hudu sun tafi, babu
abinda ya kara mana sai dai
talauci, du abinda kake da
kadara ka sayar, shekara hudu
ta tafi babu abinda suka karu sai yunwa da talauci da kara
rarrabuwar mutane da kuma

tsoro, to dayan biyu, in mun
gayara yanzu ko muyi gyaran
shekara takwas ko mu yi
gyaaran shekara hudu. Fisabilillahi, barnar da muke
ciki yanzu, muna bukatar
shekara takwas ko muna
bukatar shekara hudu mu
gyara?

Malamin ya kara da cewa duk wanda ya jawo mana shekara
hudu Allah ya la'aneshi.

Nura Hussain bayan yayi salati
ga fiyayyen halitta yace,

Ahmad Abubakar Gumi kamar
yanda kace Allah ya la'ane mu saboda muna yin Buhari to
kaine Allah ya la'ana, kai ne
la'antacce a gurin Allah, ya kara
da cewa, manzon Allah (S.A.W)

ya ce mana. La'ana tana

komawa wanda suka yi ta. Idan kayi la'ana wannan la'anar
tana tashi sama sai ta duba
taga kaine la'ananne ko kuwa
wanda ka yi wa shine
la'ananne?
Sai ta fadawa
wanda y dace, saboda haka la'antar zata koma gareka dan
baka da hujjar la'anar mu.
Ya kara da cewa, mu mun
yarda da cewa shugaba
Muhammadu Buhari
shugabane Wanda kace ya karamana talauci wannan
karya kake yi, domin talauci
dane muka san cewa muna
cikin talauci, domin bamu san
ina muka dosa ba, domin dibar
kudimmu ake ana raba muku, baka da kanti, baka da shago,

baka da sana'a, ba yanda za'ayi
kaso janar Muhammadu Buhari
saboda yace kowa saidai ya ci
guminsa.

A karshe dai yace, kamata yayi idan malamin siyasa zai yi ya
fito yayi ta karara ya dena
boye-boye..
Toh Allah ya ganar damu Hanyar gaskiya
source@ Arewamini.com.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: