A makon jiya ne jaruma Nafisa Abdullahi ta fitar da tallar wani fim dinta mai suna ‘Yaki A Soyayya’, cikin fim din wanda kamfanin Nafs Entertainment ya dauki nauyi, an nuna jarumar tana shaye-shaye, inda hakan ya sanya aka rika yamadidi da batun a kafafen sadarwa na zamani. Aminiya ta tattauna da ita kan wannan batu da ya jawo cece-ku-ce, jarumar ta yi bayanin dalilin da ya sa ta shirya fim din ‘Yaki A Soyayya’. Ga yadda hirar ta kasance:
Wata fitowa yayin xaukar fim din ‘Yaqi A Soyayya’
A makon jiya kin fitar da tallar wani sabon fim din ki mai suna ‘Yaki A Soyayya’, inda a tallar aka nuna kina shaye-shaye, hakan ya haifar da cece-ku-ce, shin da ma can kina shan sigari ne?
Wannan tambaya ta ba ni dariya, amma bari in amsa ta kai-tsaye, ba na shan taba a zahiri, na sha taba ce kawai saboda haka labarin fim din ya bukata, na sha taba ce don in nuna wa mutane illar shan kayan maye, kuma idan babu yadda za ka yi fim a kan wani batagari amma a nuna ka da siffar mutanen kirki, fim ne a kan shaye-shaye da cin zarafi, ka ga ba za a yi fim din ba tare da an nuna yadda masu shaye-shaye suke ba. Na yi hakan ne don in nuna wa mutane illar shaye-shaye da kuma cin zarafi, hakan bai dace ba.
Wannan tambaya ta ba ni dariya, amma bari in amsa ta kai-tsaye, ba na shan taba a zahiri, na sha taba ce kawai saboda haka labarin fim din ya bukata, na sha taba ce don in nuna wa mutane illar shan kayan maye, kuma idan babu yadda za ka yi fim a kan wani batagari amma a nuna ka da siffar mutanen kirki, fim ne a kan shaye-shaye da cin zarafi, ka ga ba za a yi fim din ba tare da an nuna yadda masu shaye-shaye suke ba. Na yi hakan ne don in nuna wa mutane illar shaye-shaye da kuma cin zarafi, hakan bai dace ba.
Shin me fim na ‘Yaki A Soyayya’ ya kunsa?
‘Yaki A Soyayya’ fim ne na nishadi, amma kuma ya dauki jigon illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma illar cin zarafi wanda a Turance ake kira domestic biolence.
Me ya ja hankalinki kika yi tunanin zaben jigon shaye-shaye wajen shirya fim a kansa?
A zaharin gaskiya shi ne, na taba kallon wani fim ne da aka yi a kan shaye-shaye, to fim din ya burge ni, domin kuwa ya ja hankalina sosai musamman wajen sakon da aka isar. Hakan ya sa na yi tunanin wayar da kan jama’a kan illar shaye-shaye da cin zarafin mutane ta hanyar fim.
Wane abu kike so ki cimma dalilin shirya wannan fim?
Kamar yadda na yi bayani a baya ne, ina so in fadakar da dubban matasa illar shaye-shayen miyagun kwayoyi, idan ka duba za ka ga cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na cikin manyan abubuwan da suke damun al’ummarmu, ba zai zo mini da sauki in rika bin su daya bayan daya don in wayar da kansu ba. Hanya daya da na yi tunanin fadakar da su ita ce, in shirya fim a kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi sannan in yi burin masu shaye-shaye su kalla har su daina, wadanda ba sa sha kuma su fahimci illar shan kayan maye.
Me ya sa aka sa wa fim din sunan ‘Yaki A Soyayya’?
Na dade ina tunanin sunan da zan sa wa fim din, wata rana kawai sai na ji sunan ya fado cikin raina, daga nan na sanar da wadansu a cikin Kannywood sunan, sai na ga sun yi na’am da shi, hakan ya sa ni farin ciki.
Ga shi dai fim ne a kan shan kayan maye ne, ko kin fuskanci kalubale wajen samun jaruman da suka fito a fim din?
Gaskiya ko kadan, labarin fim zan iya cewa daga wurina ya fito, amma mun rubuta labarin tare da jarumi Abdul M. Shareef, wanda shi ma ya fito a fim din, haka shi ma daraktan fim din, Alfazazee Muhammad kwararre ne, ban samu matsala da shi ba. Haka sauran wadanda na yi aiki da su, sun ba ni hadin kai domin sun fahimci cewa fim ne.
Ko wane kalubale kika fuskanta yayin daukar wannan fim din?
A gaskiya ban fuskanci matsaloli daga wurin jarumai ko darakta ko sauran wadanda na yi aiki da su ba, na fuskanci matsala ce wajen samun wurin daukar fim din, mun dauki kashi 50 cikin 100 na fim din a Abuja, amma rashin samun wurin daukar wasu fitowa da labaran fim din ya tsara sai muka tafi Jos. A Jos din ma ba mu iya karasa daukar fim din ba, saboda babu wurin da muke bukata, haka dai muka yi ta nema, inda daga karshe muka samu a Kaduna. Wannan ne kawai matsalar da na samun yayin daukar fim din.
Yanzu ga matsalar satar fasaha da ta sumar da Kannywood, yaya kike shirin yin kasuwancin fim din ke nan?
Wannan babbar tambaya ce mai wahala, amma a zahirin gaskiya ban kawo wannan a gabana ba, tsarin da na yanke shi ne in nuna fim din a sinimomi da ke jihohin Arewa, daga nan kuma sai in nuna a wasu jihohin na Kudu, kafin in yi tunanin wasu hanyoyin da zan yin kasuwancin fim din.
Yaya kike ganin za a magance satar fasaha a Kannywood?
Gaskiya satar fasaha ta yi wa Kannywood babbar illa, a gaskiya ban san ta yadda za a magance matsalar satar fasaha ba. Domin ta riga ta zama cutar sankara da ta gama cinye masana’antar, domin satar fasaha ta fi shekara 15, addu’ar da zan yi kawai ita ce, a samu sa’a gwamnati ta ji tausayinmu ta yi wani abu a kai.
Duk wanda ya kalli tallar fim din ‘Yaki A Soyayya’ ya san an kashe kudi, ko za mu iya jin nawa aka kashe wajen shirya fim din?
A yanzu ba zan iya bayyana adadin kudin da aka kashe ba, saboda kwamitin shirya fim din bai ba ni izinin haka ba, amma ina sanar da masu karatu cewa fim din yana daya daga cikin fina-finan Hausa da aka fi kashe musu kudi a tarihin masana’antar Kannywood. Na san kuma idan mutane suka kalli fim za su tabbatar da abin da na fada gaskiya ne.
A yanzu ga shi kin shirya fina-finai biyu, ba ki ganin kamar kin yi kutse a bangaren da maza ne suke da rinjiye, ba ki ganin kamar ba za ki yi nasara ba?
A wurina hakan ba damuwa ba ne, abin da na sani shi ne idan har mutum ya sa zuciya zai yi abu, to babu batun namiji ko mace, idan har mutum ya dage, ya kuma jajirce to zai samu nasara. Ba a so mutum ya sa burin yin abu sannan ya dauke shi da wasa.
Yanzu yaushe za a fitar da wannan fim mai suna ‘Yaki A Soyayya’ a kasuwa?
Za a fara nuna shi a ranar 28 ga Disamba, a gidan silimar Film House Cinema da ke Kano, kuma zan halarci silimar don in gana da masoyana. Daga nan bayan an nuna shi a silimomi sai a fitar a kasuwa.
Bayan wannan fim na ‘Yaki A Soyayya’ wane shiri kuma kike da shi nan gaba?
Bayan fim din ‘Yaki A Soyayya’ ina da wani shiri da na dade da burin shirya shi, shirin ne wanda ba a taba yin irinsa a Kannywood ba, ba zan zazzage komai yanzu ba, amma nan gaba kadan idan na fara shirya fim din kowa zai gamsu cewa ba a taba shirya irinsa a Kannywood ba.
Mene ne sakonki ga masoyanki?
Sakona shi ne ba za su ji kunya ba idan har suka kalli fim din ‘Yaki A Soyayya’, za su samu gamsuwa, sannan za su tabbatar da cewa fim din yana dauke da sakonni masu ma’ana da idan har suka kalla to ba za su yi da-na-sanin kallonsa ba. Ina yi wa masoyana fatan alheri
0 Comments:
إرسال تعليق