الاثنين، 10 ديسمبر 2018




Karanta kaji wata mata abinda ta aikata ya dauki hankalin duniya

Home › › Karanta kaji wata mata abinda ta aikata ya dauki hankalin duniya

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Wata mata ta rasu sai Mijinta ya zauna agefen kabarinta yana ta zabga kuka kuma kuka mai tsananin sai mutane suka kewaye shi suna share masa hawaye. Bayan hawayensa ya bushe sannan ya dawo hayyacinsa sai yace : Ya ku Jama'a hakika ni na yarda da mata ta,kuma ina rokon Ubangiji ya bata Aljannar Firdausi Madaukakiya Sannan ya Kara da cewa Ina rantse muku da Allah tun daga lokacin dana aureta bazan iya tuna lokacin da tayi bacci kafin nayi ba ko kuma na farka Kafin ta farka (Duk domin rarrashi gareni) Haka kuma ta kasance tana jure duk abinda nayi mata Har wayau ita ce take bude kofar gidana kafin na kwankwasa ban taba shiga gida ba face naji yana kamshin turaren Almiski ko turaren wuta. Ban taba nema tayi mini wani abu ba kama daga abinci ko waninsa face ta sadaukar da kanta wajen samar dashi domin neman yarda ta. SABODA HAKA IDONA BAI TABA AFKAWA AKANTA BA FACE NA GANTA KAMAR YADDA NAKE SO. Yaku mata wannan ya zama kalu bale agaremu shin kuna aikatawa mazajenmu abinda idan suka rasa ku ayau zasuyi irin wannan kukan? Ya Allah kabamu mata nagari masu jin taushiyin mazajensu sukuma maza Allah yabasu ikon kyautatawa matansu Ameen. Shafin komai da ruwanka, Arewabestie.blogspot.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: