[post by samaila umar lameedo]
Karanta yadda Salah ya lallasa Bournemouth
Takaitacce
14:24
Liverpool ta lallasa Bournemouth 4-0 a gida
Wasa ya kare! Liverpool ta lallasa Bournemouth a gidanta da ci hudu da ba ko daya.
14:19
Lallana ya ji ciwo
'92 Bournamouth 0-4 Liverpool
Fuskar dan wasan Liverpool Adam Lallana yana cike da jini. Wani naushi ya samu bisa tsautsayi. An dan dakatar da wasa. Amma yanzu wasan ya cigaba.
Salah ya kara!
GOAL
'77 Bournamouth 0-4 Liverpool
Salah ya ci wa Liverpool kwallo na uku a wannan wasan.
Ya yi abin da turawan Ingilishi ke ce wa hat-trick (zura kwallaye uku a raga).
Wasa kawai dan wasan Masar din yake yi da Bournemouth a yau. Ya yanke Steve Cook sannan ya kewaye Asmir Begovic, ya dawo sake yanke golwan Bournemoutha karo na biyu kuma zura kwallon a raga yayin da Nathan Ake ke kan layi ba tare da ya iya tare kwallon ba.
An kara wa Bournemouth
GOAL
'68 Bournamouth 0-3 Liverpool
Dan Bournemouth ( Steve Cook) ne ya ci kungiyarsa.
13:52
Bournemouth ta sake dabara
'65 Bournamouth 0-2 Liverpool
Ryan Fraser dai ya fara wasa ne daga baya a tsakiya. Amma yanzu ya koma ta hagu domin kai farmaki ta wurin James Milner wanda ke buga wasansa na 500, Junior Stanislas kuma ya koma dama daga hagu, yayin da David Brooks tsakiya ta gaba
13:44
Salah bai murnar ba
Mohammed Salah bai bayyana murnar cin kwaloo na biyun ba. Amma kwallayen nasa ka iya sa kungiyarsa ta yi nasara a wasan.
Fulham ta isa Old Trafford
A halin yanzu dai 'yan wasan Fulham sun isa Old Trafford don karawa da kungiyar Manchester United a wasan da za a fara karfe hudu agogon Najeriya da Nijar.
View more on Twitter
13:36
GOAL
'48 Bournamouth 0-2 Liverpool
A halin yanzu an dawo daga hutun rabin lokaci. Mohamed Salah Kuma ya kara wa Bournemouth.
13:33
Ina jin dadin aiki a Man U - Mourinho
Manajan Manchester United Jose Mourinho ya ce yana jin dadi kuma zai ci gaba da aikinsa, kamar yadda wakilinsa ya tabbatar.
Mourinho na fuskantar barazanar kora daga aikin horar da Man U yayin da kulub din ke matsayi na takwas kuma tazarar maki takwas tsakani da matsayi na hudu a teburin Premier League.
A watan Janairu Mourinho ya sabunta kwangilarsa a Old Trafford amma ana rade radin zai koma Real Madrid.
13:19
An tafi hutun rabin lokaci
HT Bournamouth 0-1 Liverpool
A halin yaznu dai an tafi hutun rabin lokaci kuma Liverpool tana gaba da Bournemouth da kwallo daya.
Idanh aka tashi haka, Liverpool za ta haye saman teburin gasar Firimiya.
13:09
Sala ya ci kwallye 40 a gasar Firimiya
View more on Twitter
A halin yanzu kwallayen da Mohamed Salah ya ci a gasar Firimiya sun kai 40.
13:01
Liverpool ta haye teburi
'31 Bournamouth 0-1 Liverpool
A halin da ake ciki yanzu dai Liverpool ta haye saman teburin gasar Firimiya.
12:59
Man City za ta ci gaba da buga Champions League
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ya samu tabbaci daga shugabbin kulub din cewa ba za a haramta masu buga gasar zakarun turai ba saboda saba dokar takaita sayen yan wasa.
12:55
GOAL
'25 Bournamouth 0-1 Liverpool
Mohamed Salah ne ya ci wa Liverpool!
12:53
Bournemouth ta fara mayar da martani
'22 Bournamouth 0-0 Liverpool
Liverpool ta dai kai wasu hare-hare daga farko, amma Bournemouth ma ta fara mayar da martani lamarin da ya sa wasan ke zafi.
Liverpool za ta iya dare wa tebur idan ta yi nasara kafin Man City ta fafata da Chelsea a Stamford Bridge
12:49
Bournemouth ta sami katin gargadi biyu
'18 Bournamouth 0-0 Liverpool
Kungiyar Bournemouth ta sami katin gargadi biyu minti 16 da fara wasa.
12:46
Ga 'yan wasan Bournemouth
Kalli 'yan wasan da ke yi wa Bournemouth wasa a yau.
View more on Twitter
12:43
Kalli yadda Liverpool suka shigo
Kalli yadda 'yan Liverpool suka shiga filin wasa.
View more on Twitter
12:38
An ture Keita
'09 Bournamouth 0-0 Liverpool
An hankade Naby Keita a wani keita da ke iya tuna wa mutane irin yadda Liverpool ta kaya da Burnley. Irin wannan wasan za a sake yi a yau?
12:34
An fara wasa
Bournamouth 0-0 Liverpool
Jama'a barkanku da shigowa wannan shafin indfa za mu kawo muku labarai da sharhi game da wasan Bournamouth da Liverpool da aka fara a halin yanzu. Dan wasan da ya fi ci wa Bournemouth kwallo, Wilson, ba zai buga ba
Milner na Liverpool zai buga wasansa na 500 a gasar Firimiya
Liverpool za ta iya haye teburin Firimiya idan ta yi nasara
Man City za ta iya karbe ragamar tebur idan ta doke Chelsea da karfe biyar
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdulwasiu Hassan da Awwal Ahmad Janyau
time_stated_uk
0 Comments:
إرسال تعليق