Ma'aikatar tsaron Amurka ta ba da kwangilar kera wa Najeriya jiragen yaki guda 12 samfurin A-29 Super Tucano.
A sanarwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron ta ce an bayar da kwangilar kera jiragen ne kan kudi dala miliyan 329 ga wani kamfanin kera jirage na Amurka Sierra Navada Corporation.
Tun a watan Afrilu ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da odar jirajen bayan doguwar tattaunawa da gwamnatin Amurka, matakin da ya kai ga sassauta dakatar da sayar wa Najeriya da makamai.
Kuma tun a watan Afrilu rahotanni suka ce gwamnatin Najeriya ta tura wa Amurka kudi dala miliyan 469, wadanda suka saba yawan kudaden kwangilar da Amurka ta sanar.
Boko Haram ta sake zama barazana - Buhari
Boko Haram 'ta kashe sojojin Najeriya 53'
Shida daga cikin jiragen za a samar da su ne dauke da wata fasahar hangen nesa, kuma da kan iya sauya bayanai zuwa bidiyo nan take.
Wani bangare na kwangilar jiragen 12, ya shafi bayar da horo ga rundunar sojin sama ta Najeriya kan shiri da kuma dubarun yaki.
Ana sa ran kammala aikin kera sabbin jiragen zuwa 2024.
Gwamnatin Najeriya ta ce jiragen za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kawo karshen yaki da Boko Haram.
0 Comments:
إرسال تعليق