[post by samaila umar lameedo]
Kotu ta ba EFCC da DSS da 'Yan sanda kwana uku su kawo Diezani
LABARAI DAGA 24BLOG
Wata babbar kotu a Abuja ta bai wa hukumar EFCC da 'yan sanda da DSS da sauran jami'an tsaron Najeriya wa'adin kwana uku su kamo tsohuwar ministar man fetur ta kasar, Mrs Diezani Alison-Madueke.
A sanarwar da mai magana da yawun hukumar EFCC Mista Tony Orilade ya aike wa manema labarai ranar Talata, ya ce mai shari'a Valentine Ashi ne ya bayar da umurnin inda ya bukaci a kama tsohuwar ministar cikin sa'o'i 72 a gurfanar da ita a gaban kotun.
Sanarwar ta ce, Kotun ta bayar da umurnin ne bayan EFCC ta bukaci kotun ta bayar da sammacin taso keyar Alison-Madueke daga Birtaniya zuwa Najeriya domin ta fuskantaci shari'a.
Tsohuwar ministar na cikin manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da ake zargi da cin hanci, ko da yake ta sha musanta zargin.
EFCC za ta gurfanar da Diezani a gaban kotu
Kotu ta ki yarda a taso keyar Diezani
EFCC ta shaida wa kotun cewa ta dade da aike wa tsohuwar ministar takardar gayyata zuwa Najeriya domin ta kare kanta daga zarge-zargen cin hancin da ake yi mata amma ta ki amsa gayyatar.
Tun da farko, EFCC ta ce a watan Fabrairun 2019 ne za a gurfanar da Misis Alison-Madueke da kuma tsohon shugaban kamfanin tatar mai na Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore kan zargin aikata laifuka biyar.
A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da karbar hanci da kyautuka a wurare biyu - duka a birnin Lagos, lamarin da ya saba wa dokar hana karbar hanci da rasha
0 Comments:
إرسال تعليق