الاثنين، 3 ديسمبر 2018




Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a,

Home Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a,

غير معرف

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]

Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a, bidiyo

LABARAI DAGA 24BLOG
A cikin faifan bidiyon, Mbaka ya dafa Obi tare da shaida ma sa cewar takarar su babu inda za ta, tamkar sun fadi zabe ne.
Mbaka ya yi magana ne cikin harshen Igbo, duk da ya kan dan tsarma da Turanci.
Majiyar legit.ng da ke fuskantar yaren Igbo ta tabbatar ma ta da cewar kalaman Mbaka ga Obi cin fuska ne.
Mbaka ya kasance daga cikin 'yan tsirarun kabilar Igbo da su ka fito fili su ka nemi jama'ar yankin kudu maso gabas su zabi shugaba a zaben shekarar 20
Sai dai a wannan karon, Limamin na darikar Katolika kuma shugaban Adoration Catholic Prayer Ministry da ke Enugu, Reverend Father Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar za su fadi sha kaye a zaben 2019.
Babban malamin addinin ya fadi hakan ne a yayin bikin baje kolin amfanin gona na 2018 a Adoration Ground da ke garin Emene.
Ya yi ikirarin cewa adduo'in da 'yan cocin adoration su kayi ne ya sanya Buhari samun nasarar zama shugaban kasa. Mbaka ya koka kan yadda shugaban kasar ya ki zuwa cocin ya yi wani aiki ko bayar da gudunmawa domin nuna godiyarsa ga Allah.
Ya kuma yi ikirarin cewa addu'o'in mabiya cocinsa ne ya warkar da shugba Buhari daga rashin lafiyar da ta same shi a shekarar 2015.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Copyright © | ArewaFresh.Com
Powered by Official ArewaFresh