Na san masu yi min fatan mutuwa — Buhari
LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ganawa da 'yan Najeriya mazauna Poland, a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce wasu masu yi masa wanna "mugun fatan na mutuwa" har sun fara neman mukamin mataimakin shugaban kasa, idan Osinbajo ya zama shugaban kasa.
Kun san cutar da ke damun Muhammadu Buhari?
Ana zuzuta rashin lafiyar mijina — Aisha Buhari
"Mutane da dama sun dauka cewa zan mutu a lokacin da na yi rashin lafiya. Wasu daga cikin su sun rika zuwa wurin mataimakin shugaban kasa suna kamun kafa domin ya ba su mukamin mataimakin shugaban kasa saboda sun dauka na riga na mutu," in ji Buhari.
Ya ce "amma mutumin ya ji kunya, kuma har ma ya ziyarce ni a London lokacin da na ke samun sauki."
Buhari dai na fadar haka ne lokacin da ya ke amsa tambayar wani dan Najeriya da ya tambaye shi ko shi ne Buharin ainihi na Daura ko kuwa wani ne aka kawo daga Sudan ya ke kwaikwayonsa?
Wasu 'yan kasar dai musamman a yankin kudancin kasar na yada jita-jitar cewa Buhari na Najeriya ya jima da mutuwa, don haka wani ne yake kwaikwayonsa, ana yi wa 'yan Najeriya "angulu da kan zabo."
To sai dai a amsar da ya bayar Buhari ya ce "ni ne na ainihi, ina tabbatar muku da haka. Kuma nan ba da jimawa ba zan yi bikin cikar shekara 76 a duniya, kuma zan kara karfi.
Shugaban ya soki masu yada wannan jita-jita, inda ya ce "ba su san ya kamata ba, kuma abu ne da ya sabawa koyarwar duk wani addini".
Wannan ne karon farko da shugaba Buhari da gwamnatinsa ke maida martani kan kalaman da ake yi cewa ba Buhari na ainihi ne ke mulkin Najeriya ba.
0 Comments:
إرسال تعليق