[post by samaila umar lameedo]
'Najeriya ta sayi sabbin jiragen yaki 18 don yakar Boko Haram'
LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar sojin sama ta Najeriya na jiran isowar wasu sabbin jiragen yaki guda 18 domin yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi.
Babban hafsan sojin sama na kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce suna jiran isowar jiragen yaki shida masu saukar angulu daga Italiya da kuma wasu jiragen soji guda 12 daga Amurka
Jaridun kasar sun ambato shi yana tabbatar da haka a yayin bude wani sabon dakin tiyata na zamani a asibitin sojin sama da ke Kano.
Ya ce jiragen za su taimaka wajen murkushe Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma masu satar mutane a sassan arewacin kasar.
Amurka na shirin kera wa Najeriya jiragen yaki 12
Boko Haram ta sake zama barazana - Buhari
Tuni ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da ba da kwangilar kera wa Najeriya jiragen yaki guda 12 samfurin A-29 Super Tucano.
Tun a watan Afrilu ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da odar jirajen bayan doguwar tattaunawa da gwamnatin Amurka, matakin da ya kai ga sassauta dakatar da sayar wa Najeriya da makamai.
Ana sa ran kammala aikin kera sabbin jiragen zuwa 2024.
Gwamnatin Najeriya ta ce jiragen za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kawo karshen yaki da Boko Haram.
0 Comments:
إرسال تعليق